Masuntan da suka tsinci dutse mai darajar naira miliyan 615 a cikin giwar teku a Yemen

Bayanan bidiyo, Masuntan da suka tsinci dutse mai darajar miliyan N615m a Yemen
An wallafa

Wasu masunta a kasar Yemen sun ga gawar giwar teku tana yawo a kan Kogin Aden.

Sun gano wani dutse mai darajar $1.5m kwatankwacin N615m a cikinta wanda kudinsa ya fitar da su daga talauci da kuma taimaka wa mutanen kauyensu.

Dutsen ambar, da ake samu a cikin giwar teku, dutse ne mai daraja da ake amfani a kamfanonin yin turare da zummar sanya kanshinsa ya dade bai gushe ba.

Masu daukar bidiyo: Eloise Alanna, Suaad Al-Salahi da Adnan Ameen Al-Haaj.