Ana kokarin rufe bakin 'yan jarida kan rikicin Isra'ila da Falasdinawa - Kungiyoyi
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Kungiyoyin kare hakkin 'yan jarida sun yi Allah-wadai da harin da Isra'ila ta kai Gaza, wanda ya lalata wani katafaren bene mai dauke da ofisoshin kamfanin dillancin labarai na Associated Press AP, da Al Jazeera.
Harin ya zo ne a yayin da aka rufe shingayen binciken ababen hawa, sannan aka hana 'yan jaridar kafofin yada labaran kasashen waje shiga Gaza.
Isra'ila ta yi zargin cewa hukumar leken asirin dakarun Hamas na ayyukanta daga cikin ginin, amma babban editan AP ya yi kira da a kaddamar da bincike kan harin.