Rabi'u Kwankwaso: Kalli bidiyon tsohon gwamnan Kano kan filayen da ake zargin Ganduje na sayarwa
An wallafa
Tsohon Gwamnan jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya soki lamirin gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje game da shirin gwamnatinsa na karbar rancen naira biliyan ashirin don aiwatar da aikin gina gada a birnin Kano.
Sanata Kwankwaso ya ce ba daidai ba ne gwamnati ta ci bashin da zai bar al`ummar da za a haifa nan gaba da dawainiyar biya.
A tattaunawarsa da BBC, tsohon gwamnan Kanon ya ce hakkin gwamnatin tarayya ne ta gina gadar, wadda ta hada birnin Kano da hanyar zuwa Wudil.