Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Abdulwadud Harun Attijjaniy
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A cikin shirinmu na Ku San Malamanku na wannan makon, a wannan makon mun tattauna da shugaban gudanarwar darikar Tijjaniyya a kasar Ghana Sheiekh Abdulwadud Harun Attijjaniy
Malamin ya bayyana cewa an haife shi a darikar Tijjaniyya ya kuma taso a cikinta, sannan ya yi rubuce-rubuce a kanta.
Ya ce ya shiga kauyuka da birane domin yada addinin Musulunci da darikar ta Tijjaniyya.
Sheikh Harun ya ce a Ghana akwai fahimtar juna tsakanin kungiyoyin Musulmin kasar, haka kuma suna zaman lafiya da mabiya wasu addinan.