Abubuwan da ya kamata ku sani kan ciwon Ƙoda
An wallafa
Latsa alamar lasifikar domin kallon bidiyon
Yau ce ranar Ƙoda ta duniya wadda hukumar Lafiya ta Duniya ta keɓe don nusar da jama'a kan muhimmancin lafiyar ƙoda.
Alƙaluma sun nuna cewa cikin duk mutum 9 a kan samu ɗaya da ke fama da larurar ƙoda.
Wani nazari da aka yi a 2019 ya nuna cewa a duk mako, mutum 5 kan mutu yayin jiran dashen ƙoda.
Taken ranar a bana shi ne "zama cikin ƙoshin lafiyar ƙoda".
Girman matsalar ƙoda a Najeriya
Dr Aisha Nalado, wata likitar koda a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano da ke jihar Kano ta bayyana cewa "a cikin kashi 100 za a ce kashi 20 na mutane suna ɗauke da cutar ƙoda".
Ta bayyana cewa cutar ta ƙoda tana iya kama kowa daga manya har ƙanana - a kowane lokaci na rayuwa za a iya samun cutar ƙoda.