Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Dr Jabir Sani Maihula
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
An haifi Sheikh Jabir Sani Maihula ranar Juma'a 3 ga watan Yulin shekarar 1981 a garin Sifawa da ke jihar Sokoto.
Ya fara karatun addini wajen mahaifi da mahaifiyarsa a gida na Fiƙihun Malikiyya da Iziyya da Ahalari, sannan ya halarci makarantar addini da ke cikin gidansu inda ya karanci Ƙur'ani da Hadisi.
Ya kuma halarci makarantar soro wajen Malam Ibrahim Auro. Ya yi makarantar firamare a Sokoto sai sakandare ta Kwalejin Fasaha ta Rinjin Sokoto.
Bayan nan sai ya samu gurbin yin digiri A Madina a shekarar 1999, amma sai da ya fara koyon Larabci na tsawon shekara ɗaya. A lokacin shi ne ɗalibi mafi ƙarancin shekaru Najeriya.