Yadda za ku buɗe shafin BBC Hausa na intanet a kan Opera Mini

Bayanan bidiyo, Bidiyo: Yadda za ku buɗe shafin BBC Hausa na intanet a kan Opera Mini
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A ƴan kwanakin nan masu bibiyar shafin www.bbchausa.com da dama a kan mahnajar Opera Mini a intanet ba sa iya buɗe shi, ko kuma idan sun buɗe ba sa iya ganin labaran da ke kansa.

Wannan na faruwa ne saboda wasu matsaloli na na'ura.

Sai dai BBC Hausa ta samo muku mafita dangane da hakan, ta yadda za ku iya ci gaba da buɗe shafin ba tare da wata tangarɗa ba, da samun damar ci gaba da karanta labaran da muke wallafa muku.

Ga matakan da za ku bi dalla-dalla

1. Idan kuka sanya adireshin www.bbchausa.com a shafin Opera Mini za ku ga ya nuna fari babu komai a kai.

2. Sai ku je can kasan shafin inda za ku ga tambarin Opera Mini da launin ja, sai ku latsa shi.

3. Daga nan zai shigar da ku wajen da za ku ga "settings"

4. Bayan kun shiga settings ɗin sai ku dinga duba rubutun har ku zo kan "Data Savings."

5. Bayan kun shiga "Data Savings" za ku ga inda aka rubuta "automatic" sai ku latsa gefensa.

6. Daga nan za ku ga an sa automatic da "high" da kuma "off". Sai ku latsa "high" din ko "off".

7. Sai ku koma baya wajen ainihin shafin ku sabunta shi, wato "refreshing."

8. Shi kenan za ku ga shafin www.bbchausa.com ya buɗe da labaran da aka wallafa.