Abdulaziz Yari: Za mu sake kafa gwamnati a jihar Zamfara a 2023

Bayanan bidiyo, Hirar BBC da Abdul'aziz Yari tsohon gwamnan Zamfara
An wallafa

Latsa hoton sama domin kallon hirar

Tsohon gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar ya ce APC ta sasanta da ɓangarorinta da ke rikici domin kafa gwamnati a 2023.

A hirarsa da BBC ya ce yanzu an fahimci juna tsakaninsa da bangarorin Jam'iyyar APC da ke rikici kuma sun yadda kaddara ce ta fada wa jam'iyyar a zaɓen 2019.

Rikicin jam'iyyar APC a Zamfara ne ya sa Jam'iyyar PDP ta tsinci dami a kala sakamakon hukuncin kotun koli da ya soke dukkanin kujerun da jam'iyyar APC ta lashe a jihar a zaben 2019.