Indiya: Matar da ta tara ƙwanji saboda cimma burin rayuwa

Bayanan bidiyo, Indiya: Matar da ta tara ƙwanji saboda cimma burin rayuwa
An wallafa

Latsa alamar lasifika a hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

A lokacin da Kiran Dembla ta fara rashin lafiya sakamakon taruwar jini a ƙwaƙwalwarta, matar aure ce ita wacce ke kula da hidimar gida da ta iyali kawai a Indiya.

Ta warke daga cutar da ta yi mata barzanar, amma magungunan da ta dinga sha sun sa ta ƙara lafta ƙiba.

Daga nan ne fa Kiran ta ɗaura ɗamarar rage ƙibar tare da sauya akalar rayuwarta.

A yanzu a matsayinta ta ɗaya daga cikin mata ƙalilan masu aikin tara ƙwanji a Indiya, ta zama mai yi wa fitattun mutane horo kan gina ƙwanji.