Donal Trump: Yadda za ka zama tsohon shugaban ƙasa
An wallafa
A yau ne Donald Trump zai bar fadar White House a matsayinsa na shugaban Amurka bayan cikikar wa'adinsa.
Sai dai bai kamata ya damu ba saboda barin ofishin shugaban Amurka da ake cewa Oval Office na zuwa da wasu alfarmomi ciki har da maƙudan kuɗaɗe da jami'an tsaro, da ba da bayanan sirri har ma da taimako wajen aike wa da sakonni.