EndSARS: Mece ce gaskiyar abin da ya faru a Lekki?

Bayanan bidiyo, EndSars: Mece ce gaskiyar abin da ya faru a Lekki?
An wallafa

Matasan Najeriya sun yi huɓɓasa a shekarar 2020 inda suka shirya zanga-zangar End Sars ta nuna adawa ga cin zarafin da suka ce 'yan sanda na yi masu.

Matasan sun yi wa kansu inkiya da matasan "Soro Soke" - wanda ke nufin "masu ɗaga murya" a yarabanci, kuma sun yi tattaki a titunan ƙasar tsawon mako biyu suna neman sauyi.

Tattakin nasu ya zo ƙarshe ne ranar 20 ga watan Oktoba lokacin da sojojin ƙasar suka buɗe wa masu zanga-zangar lumanan wuta, a wata unguwar masu hannu da shuni a Legas.

Wakiliyar BBC Mayeni Jones ta gudanar da bincike kan abin da ya faru a wannan dare da kuma halin ɗar-ɗar ɗin da jama'a suka shiga bayan harbe-harben na Lekki.