Bidiyon yadda magoya bayan Trump suka mamaye majalisar Amurka
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Wani zaman hadaka na majalisun dokokin Amurka da zai tabbatar da zaben Joe Biden ya katse zamansa bagatatan, sannan an rufe ginin majalisar Capitol Hill, bayan magoya bayan Donald Trump sun kusta cikin ginin.
Tun da farko Shugaba Trump ya yi wa magoya bayansa jawabi a wajen wani gangami a wajen White House sannan ya nemi su nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓen.