Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Nur Arzai

Bayanan bidiyo, Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Nur Arzai
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Ɗaya daga cikin fitattun malaman addinin Musulunci a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya Sheikh Muhammad Nur Muhammad Arzai, ya ce babu abin da ya fi farin ciki da shi a rayuwarsa fiye da kasancewarsa shi da ƴaƴansa har da wasu jikokinsa koyarwa suke yi.

Sheikh Nur Arzai shi ne limamin Masallacin Juma'a na Sunusi Dantata da ke Kofar Ruwa a Kano, ya ce ya buɗe makarantu da dama musamman don koyar da yara ƙanana, kuma a yanzu ma yana da burin buɗe wasu ƙarin makarantun a wasu jihohin Najeriya inda za a ringa karantar da yara addinin Musulunci.

Sheikh Nur Arzai wanda yana ɗaya daga cikin manyan jigogin ɗariƙar Tijjaniya a Kano, ya bayyana haka ne a cikin shirin Kusan Malamanku na BBC Hausa, lokacin da yake bayani kan iyalensa.

Ɗaukar bidiyo da tacewa: Yusuf Ibrahim Yakasai