...Daga Bakin Mai Ita tare da Sani TY Shaban 'Free Boy'

Bayanan bidiyo, ...Daga Bakin Mai Ita tare da Sani TY Shaban 'Free Boy'
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Free Boy yana daga cikin mawakan Hip Hop na Hausa da suke tasowa.

A shirin Daga Bakin Mai Ita Kashi na 26, mun kawo hira da Free Boy daya daga cikin mawakan Hip Hop na Hausa da suke tasowa.

Ya ce ya fara waka ne bayan da ya kalli wata hira ta talabijin da aka yi da wani yaro mawaki Lil Ameer gabanin muutuwarsa.

Ya ce ya kara son wakar bayan mutuwar Lil Ameer.

Sani TY Shaban ko kuma Free Boy, wanda mahaifinsa ma mawaki ne ya ce yana samun goyon baya daga iyayensa.

Ya ce ko da ya kammala karatu ya kuma samu aiki zai ci gaba da waka saboda ya dauke ta abin sha'awa, ba wai sana'a ba.

A yanzu haka yana aji biyu na makarantar sikandare.