Mata 100: Shari'ar kisan da ƴan mata uku suka yi wa mahaifinsu da ta girgiza Rasha
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Shari'ar da ake yi ta zargin wasu ƴan mata uku da kashe mahaifinsu ta girgiza Rasha.
An kama Krestina da Angelina da Maria Khachaturyan bayan da mahaifinsu ya mutu sakamakon raunukan da ya ji, bayan kai masa hari da wuƙa da guduma.
Sun ce sun shafe shekaru mahaifinsu suna fuskantar cin zarafi a hannun mahaifinsu.
Ra'ayi ya rarrabu inda wasu ke ganin yaran sun yi hakan ne a matsayin kare kai, wasu kuma na cewa kisan kai ne da gangan.
Lamarin ya fito da yadda ake samun matsalar cin zarafi a gidaje a Rasha; a cewar ma'aikatar harkokin cikin gida inda ta ce kashi 40 cikin 100 na laifukan da ake yi ana yin su a cikin.