Ethiopia: Kalli lokacin da aka kai mummunan hari babban birnin Tigray a Habasha
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Hukumomin tarayyar Habasha sun musanta rahotannin da ke cewa fararen hula aka so kai wa harin sama a babban birnin yankin Tigray.
Sun ce an kai harin ne da nufin samun mayaƙan ƙungiyar TPLF.
Wani mummunan harin sama da aka kai ranar Talata ya hallaka mutum biyu tare da ji wa wasu da dama rauni a Mekelle.
Har yanzu ba a tabbatar da wanda ya kai harin ba.