Coronavirus: Ga matasan da ke so a shafa musu cutar don yin gwajin riga-kafi a kansu
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Za ku yarda a shafa muku cutar corona? Duk da sunan kimiyya. Akwai mutane da dama da za su yarda, har ma kuma suna wata fafutuka mai taken 1 Day Sooner, don a bar su su shiga cikin waɗanda za a yi gwajin riga-kafi a kansu, don a yi gaggawar samar da shi.
Mun yi magana da shida daga cikin waɗannan masu aikin sa kan daga sassan duniya daban-daban, waɗanda suke ganin ba sa fuskantar haɗarin kamuwa da cutar kuma suna son taimakawa.
Amma me ake nufi da gwajin riga-kafi a kan ɗan adam, kuma mene ne haɗarin da ke tattare da hakan?