Gasar Hikayata: Shawarwari kan yadda ake rubuta gajerun labarai daga Fauziyya D. Sulaiman
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A yayin da ya rage 'yan makwanni a rufe shiga Gasar Hikayata ta BBC hausa ta shekarar 2020, mun tsara gabatar muku da wannan bidiyo domin ba ku ƙarin haske kan yadda za ku shiga gasar.
A cikin wannan bidiyon, marubuciya Fauziyya D Sulaiman ta bai wa mata shawarwari kan yadda ake rubuta gajerun labarai, musamman ga masu sha'awar shiga Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2020.