Coronavirus a Kano: Har yanzu ina shan tsangwama kan zargin kai cutar
An wallafa
Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Mutumin da aka yi zargin cewa shi ne na farko da ya kamu da cutar korona a Kano, ya ce bai ji daɗin yadda aka yi ta yayata cewa shi ne ya kai cutar jihar ba.
Ambasada Kabiru Rabi'u wanda yanzu ya warke har ma an sallame shi daga asibiti, ya sha kakkausar suka da miyagun kalamai har da tsinuwa bisa zargin cewa ya kai korona jihar Kano da gangan.
Daukar bidiyo: Khalifa Shehu Dokaji
Tace bidiyo da tsara shi: Fatima Othman