Abin da ya sa na ajiye rawanina — Naziru 'Sarkin Waka'
An wallafa
Latsa bidiyon sama domin kallo
Shahararren mawakin nan Naziru M Ahmad, ya bayyana mana abin da ya sa ya sauka daga mukaminsa na Sarkin Wakar Sarkin Kano.
Mawakin ya ce ya sauka ne saboda sarautar tasa na da alaka da wanda ya nada shi, wato tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II.
A makon jiya ne gwamnatin jihar Kano ta sauke Muhammadu Sanusi na II daga kan mulki bayan ta zarge shi da rashin biyayya.
Daga nan ne aka kai tsohon sarkin jihar Nasarawa amma daga bisani kotu ta umarci a sake shi inda ya tafi birnin Lagos.
Naziru M. Ahmad dai shi ne ya wake tsohon sarkin Kano Sanusi na II a cikin fitacciyar wakarsa ta 'Mata ku dau turame'.