Kociyan Burnley, Vincent Kompany ya zama wanda zai ja ragamar Bayern Munich, wadda ta yi fama da kalubale a kakar bana.
Tuni kuma ya amince da ƙunshin ƙwantiragin da zai kare a karshen kakar 2027, ya maye gurbin Thomas Tuchel.
Ƙungiyar dake buga Bundesliga ta nemi wanda zai maye gurbin Tuchel, wanda cikin Fabrairu ya sanar da zai ajiye aikin da zarar an kammala kakar nan.
Kociyan Bayer Leverkusen, Xabi Alonso da na tawagar Jamus, Julian Nagelsmann da na Austria, Ralf Rangnick duk sun ki amincewa da tayin da aka yi musu.
Haka kuma an kasa rarrashin Tuchel ya sauya shawara, amma hakan bai yiwuba, hakan ya sa ƙungiyar take ta neman kociyan da ya kamata ta dauka.
Kompany ya taka rawar gani a lokacin da ya horar a Anderlecht da kuma Burnley, wadda ya kai gasar Premier League a bara daga Championship a kakar farko.
Ko da yake ta kasa taka rawar gani a babbar gasar tamaula ta Ingila ta bana, wadda ta kare a mataki na biyun karshe, ke nan za ta koma buga Championship a badi.
Haka kuma ƙungiyar dake buga Bundesliga na tuna rawar da ɗan kwallon ya taka a Hamburg lokacin da yake taka leda, sannan yana jin harshen Jamus.
Bayern Munich ta karkare kakar bana ba tare da lashe kofi ba karkashin Tuchel da yin ta uku a teburin Bundesliga da Leverkusen ta lashe, Stuttgard ta yi ta biyu.