Hukumar Premier League na gudanar da bincike kan Chelsea
Hukumar kula da gasar Premier tana binciken yuwuwar keta ka'idojin hada-hadar kudi kan Chelsea.
Hukumar Uefa ta ci tarar Chelsea fam miliyan 8.6 a watan Yuli saboda karya ka'idar hada-hadar kudi na Financial Fair Play sakamakon ba da bayanan kudi da ba su cika ba tsakanin 2012 da 2019.
Sabbin mamallakan kungiyar ta Stamford Bridge ne suka ruwaito wadannan bayanan bayan da aka sayar kungiyar a watan Mayu.
An fahimci sun kuma sanar da hukumar Premier League kan batutuwa makamantan haka.
A yanzu hukumar tana nazarin yiwuwan gabatar da takamammen tuhuma, kamar yadda aka yi wa Manchester City da Everton.
Tarar farko da aka ci kungiyar ta shafi tsawon shekaru bakwai lokacin da Roman Abramovich gudanar da harkokinta.
Abramovich ya sayar da Chelsea ga wata kungiya karkashin jagorancin Ba'amurke Todd Boehly da kuma kamfanin Clearlake Capital mai zaman kansa.
Ana iya cin tarar kungiyoyi tare da cire musu maki idan aka same su da laifin karya dokokin hada-hadar kudi.