Hukumar Premier League na gudanar da bincike kan Chelsea

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Hukumar Premier League na gudanar da bincike kan Chelsea

    Chelsea FC

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da gasar Premier tana binciken yuwuwar keta ka'idojin hada-hadar kudi kan Chelsea.

    Hukumar Uefa ta ci tarar Chelsea fam miliyan 8.6 a watan Yuli saboda karya ka'idar hada-hadar kudi na Financial Fair Play sakamakon ba da bayanan kudi da ba su cika ba tsakanin 2012 da 2019.

    Sabbin mamallakan kungiyar ta Stamford Bridge ne suka ruwaito wadannan bayanan bayan da aka sayar kungiyar a watan Mayu.

    An fahimci sun kuma sanar da hukumar Premier League kan batutuwa makamantan haka.

    A yanzu hukumar tana nazarin yiwuwan gabatar da takamammen tuhuma, kamar yadda aka yi wa Manchester City da Everton.

    Tarar farko da aka ci kungiyar ta shafi tsawon shekaru bakwai lokacin da Roman Abramovich gudanar da harkokinta.

    Abramovich ya sayar da Chelsea ga wata kungiya karkashin jagorancin Ba'amurke Todd Boehly da kuma kamfanin Clearlake Capital mai zaman kansa.

    Ana iya cin tarar kungiyoyi tare da cire musu maki idan aka same su da laifin karya dokokin hada-hadar kudi.

  2. Burnley ta dauko Berge daga Sheffield United

    Sander Berge

    Asalin hoton, Getty Images

    Burnley ta sayi dan wasan tsakiya Sander Berge daga Sheffield United kan kudi fan miliyan 12.

    Dan wasan mai shekaru 25 dan kasar Norway ya koma kan kwantiragin shekaru hudu a Turf Moor kuma ya zama dan wasan na 11 da kocin Burnley Vincent Kompany ya dauko a bazaran nan.

    Berge ya koma Blades ne daga Genk a shekarar 2020 kan kudi fam miliyan inda ya buga wasanni 109.

    Berge ya fara wasa a bangaren matasa ta kungiyar Asker ta Norway kuma ya sami komawa Valerenga a babban matakin kasar a 2015, kafin ya koma kulob din Belgium Genk a 2017.

    Ya shiga shekarar karshe a kwantiraginsa a Bramall Lane kuma shi ne babban dan wasa na biyu da ya bar Sheffield United a bazara bayan da dan wasan tsakiya Iliman Ndiaye, mai shekara 23, ya koma Marseille.

  3. Weghorst ya koma Hoffenheim akan aro

    Weghorst

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan Burnley Wout Weghorst ya koma Hoffenheim ta Bundesliga a matsayin aro na kakar 2023-24.

    Weghorst, mai shekaru 31, ya shafe rabin kakar wasan da ta gabata a matsayin aro a Manchester United, inda ya lashe kofin Carabao a watan Fabrairu kuma ya zura kwallaye biyu.

    Lokaci na karshe da ya buga a Jamus, kafin ya koma Burnley, shi ne Wolfsburg. A lokacin, dan wasan na Netherlands ya ci kwallaye 70 a wasanni 144.

  4. Wrexham ta cire Wigan Athletic a Carabao cup

    Wrexham Athletic

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabbin zuwa gasar League Two, Wrexham sun fitar da Wigan Athletic daga gasar Carabao da ci 4-2 a bugun fanariti.

    Bangarorin biyu sun kasa samun nasara cikin mintuna 90 a filin wasa na Stok Racecourse inda wasan ta kare a kunnen doki, kuma kai tsaye aka nufi bugun fanareti.

    'Yan wasan Wigan Charlie Hughes da Thelo Aasgaard ne suka zubar da bugun daga kai sai mai tsaron gida inda suka baiwa Wrexham nasara.

    Dragons sun tsallake zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin EFL a karon farko tun 2007.

  5. Ross Barkley ya koma Luton Town

    Ross Barkley

    Asalin hoton, gett

    Tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila, Ross Barkley, ya koma kungiya ta firimiya, Luton Town a matsayin kyauta.

    Dan wasan mai shekaru 29, wanda ya buga wa kasarsa wasa sau 33, yakoma kungiyar ne bayan ya bar kulob din Nice na Ligue 1 a bazara.

    A ranar Asabar ne kungiyar da ta hauro zuwa gasar Firimiya a kakar wasan da ta gabata za ta buga wasanta na farko a kara wasan bana inda za ta ziyarci da Brighton.

    Barkley ya buga wasanni sama da 200 a matakin farko a kulob din Everton da Chelsea da Aston Villa kuma ya buga wa Ingila wasa a gasar cin kofin duniya ta 2014.

  6. Man City na Zawarcin Paqueta daga West Ham

    Lucas Paqueta

    Asalin hoton, getty

    Manchester City na zawarcin dan wasan tsakiyar West Ham Lucas Paqueta.

    Dan kasar Brazil ya koma Hammers ne daga Lyon kan fan miliyan 36.5 a bazarar da ta wuce kuma ya taka rawar gani yayin da kungiyar ta lashe gasar cin kofin Europa.

    Ba a tunanin City ta yi tayin neman Paqueta tukuna.

    Sai dai mai yiyuwa ne za su gwada kudurin West Ham yayin da Pep Guardiola ke neman karfafa ‘yan wasansa bayan nasarar da suka samu a kakar wasa da ta gabata inda su ka lashe manya gasanni guda uku.

    West Ham za ta yi jinkirin rasa wani babban jigo a cikin tawagar David Moyes bayan ficewar Declan Rice zuwa Arsenal kan fan miliyan 105.

    Paqueta ya na da shekaru hudu a kan kwantairagin da ya sanya hannu a kai a bazarar da ta gabata.

  7. Wolves ta nada Gary O'Neil sabon kocinta

    Gary O'Neil

    Asalin hoton, Getty Images

    Wolverhampton ta sanar da nada tsohon kociyan Bournemouth, Garry O'Neil, a matsayin wanda zai horar da ita.

    Tuni ya amince da kwantiragin kaka uku, ya kuma maye gurbin Julen Lopetegui.

    An sanar da raba gari tsakanin kungiyar da Lopetegi a Molineu ranar Talata, kwana uku kafin fara kakar Premier League ta 2023/24.

    O'Neil ya ja ragamar Bournemouth zuwa mataki na 15 a teburin Premier League a bara, daga baya ta kore shi ranar 19 ga watan Yuni.

    Mai shekara 40, shi ne kociyan Wolves na hudu cikin shekara biyu.

    Zai fara aiki ranar Litinin, lokacin da Wolves za ta ziyarci Old Trafford domin karawa da Manchester United a wasan farko na Premier League.

  8. Iniesta ya koma kungiyar Emirates

    Andreas Iniesta

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon dan wasan Barcelona Andres Iniesta ya kulla yarjejeniya da kungiyar Emirates Club ta gasar United Arab Emirates Pro League.

    Dan kasar Sifaniyan ya bar kungiyar Vissel Kobe ta kasar Japan a tsakiyar kakar wasannin J-League ranar 1 ga watan Yuli.

    Dan wasan mai shekaru 39, ya buga wasanni 134 a kulob din na Japan, inda ya lashe Kofin Emperor's Cup a shekarar 2019 da kuma Super Cup na Japan a shekarar da ta biyo baya.

    Kungiyar Emirates, wacce ta yi nasara a gasar ta UAE a kakar wasan da ta wuce, ta buga "maraba da Iniesta" a shafukanta na sada zumunta.

    Iniesta ya koma Japan ne bayan ya shafe shekaru 22 yana taka leda a Barcelona, ​​inda ya lashe kofuna 32 kuma ya buga wasanni 674.

    Ya lashe wasanni 133 tare da kasar Sifaniya kuma ya taimakawa kasar ta lashe gasar cin kofin duniya ta 2010 da kuma gasar cin kofin nahiyar Turai a 2008 da 2012.

    Sabon kulob din nasa za ta fara kakar wasan bana da Al-Wasl a ranar 19 ga watan Agusta.

  9. Wolves ta sallami Lopetegui

    Julen Lopetegui

    Asalin hoton, getty

    Kocin Wolves Julen Lopetegui ya bar kungiyar, inda tsohon kocin Bournemouth Gary O'Neil zai maye gurbinsa.

    Wolves ta dade da sanin cewa Lopetegui, mai shekaru 56, yana son barin kungiyar.

    Wolves ta ce dukkan bangarorin biyu sun amince da sabanin ra'ayi kan wasu batutuwa kuma sun amince cewa kawo karshen kwantiraginsa cikin aminci shine mafita mafi kyau".

    Wolves ta sanar da barin kocin dan Sifaniya kwanaki uku kafin a fara gasar Premier - za su kara da Manchester United ranar Litinin.

    Kulob din ta ce "an ci gaba da tattaunawa a cikin 'yan makonnin nan, don bai wa kulob din lokaci ta yi aiki kan neman wanda zai maye gurbin Lopetegui da ma'aikatansa don tabbatar da cewa 'yan wasa na cikin kyakkyawan yanayi don sabuwar kakar wasa.

    Wakilin wasanni na BBC Simon Stone ya fahimci cewa an rufe yarjejeniyar rabuwa tyun lokacin da aka yi wasan sada zumunta da Celtic a watan jiya, amma Lopetegui ya amince ya ci gaba da ba da lokaci don nemo wanda zai maye gurbinsa.

    An dauki 'yan takara da dama a matsayin wadanda za su maye gurbin Lopetegui amma O'Neil mai shekaru 40 ya burge shugabannin kuma ana sa ran za a tabbatar da shi a matsayin sabon kocin ranar Laraba.

  10. Barcelona ta lashe Kofin Joan Gamper

    Barcelona

    Asalin hoton, Getty Images

    Barcelona ta doke Tottenham 4-2, wanda hakan ya sa kungiyar ta dauki kofin Joan Gamper, a wani bangare na shirye-shiryen kungiyoyin biyu na tunkarar kakar wasa ta 2023-24.

    Robert Lewandowski ne ya ci wa kungiyar ta Catalonia kwallo ta farko kafin daga bisani Oliver Skipp ya zura kwallo biyu a ragar Barcelona.

    Daga baya Ferran Torres da Ansu Fati ne suka saka bangaren Xavi a gaba, kafin Abde Ezzalzouli ya kara ta hudu.

    Wadannan kwallayen sun tabbatar da cewa Barcelona ta lashe gasar share fagenta da aka saba na shekara ta 11 a jere.

  11. West Ham ta kammala cinikin Maguire da Ward-Prowse

    Harry Maguire

    Asalin hoton, Getty Images

    West Ham United ta amince da cinikin Harry Maguire na Manchester United da James Ward-Prowse na Southampton kan kudi kusan fan miliyan 60 gaba daya.

    Ana tunanin kowace yarjejeniya zata kai £30m.

    Maguire, mai shekaru 30, ya yi fama da samun damar buga wasa a Old Trafford a kakar wasan da ta wuce kuma an cire shi daga mukamin kyaftin a kakar wasa ta bana.

    An fahimci cewa yana sha'awar tafiya duk da cewa ba a kammala kulla yarjejeniyar sharudda ba, amma ba a tsammanin hakan zai zama matsala.

    Maguire ya koma United ne a watan Agustan 2019 kan fam miliyan 80, wanda shi ne dan wasan baya da ya fi tsada a duniya.

    West Ham dai na ta kokarin daukar Ward-Prowse a bazaran nan amma Southampton, wacce ta koma gasar Championship a kakar da ta gabata, ta ki amincewa har zuwa wannan lokacin.

    Sai dai da alama cewa babu makawa Southampton ta rasa kyaftin din ta kuma yanzuyafiyarsa ta kusa tabbata.