Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Al Hilal ta Saudiyya ta taya Mbappe kan fan miliyan 259

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.

Rahoto kai-tsaye

  1. Boga na shirin komawa OGC Nice

    Dan wasan gefe na Atalanta Jeremie Boga yana gab da komawa kungiyar OGC Nice ta Faransa akan kusan Yuro miliyan 20.

    A cewar majiyoyi daban-daban yarjejeniyar tana mataki na karshe kuma ana kan tattaunawa tsakanin kungiyoyin biyu.

    Ana sa ran gabaɗayan farashin cinikin zai kai kusan Yuro miliyan 20. Wannan yana kusa da €22m da aka biya don siyan shi daga Sassuolo a 2022.

    Boga ya kasance tsohon dan wasan bangaren matasa na Chelsea, ya tafi aro a Renne da Granada da Birmingham kafin a sayar da shi kan farashin €10m ga Sassuolo a 2018.

    Yanzu yana da shekaru 26 kuma ya bugawa Ivory Coast wasanni 12 , inda ya zura kwallo daya a raga.

  2. West Ham na zawarcin Origi

    Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta West Ham United tana dab da kammala cinikin dan wasan gaba na AC Milan Divock Origi.

    Dan wasan na kasar Belgium ba yi kokari ba a San Siro tun bayan da ya koma daga Liverpool shekara daya da ta wuce, amma har yanzu anan kallonsa a matsayin gwarzo a tsakanin magoya bayansa a Anfield.

    Origi ya lashe gasar Premier da gasar zakarun Turai a lokacin da ya ke wasa a Liverpool, inda ya kware ta fannin zura wasu muhimman kwallaye a manyan wasanni kamar shahararrun wasannin da suka buga da Barcelona da kuma Tottenham a shekarar 2019.

    Origi yanzu zai iya komawa Ingila, inda ake ganin an kusa kulla yarjejeniya tsakanin Milan da West Ham.

    Hammers na buƙatar ƙarin inganci a 'yan wasan gana ta kuma Origi zai kasance zaɓi mai kyau a halin da ake ciki ganin cewa ba zai yi tsada sosai ba..

  3. Hislop ya farfado bayan ya yanki jiki ya fadi

    Tsohon golan West Ham Shaka Hislop ya dawo cikin hayyacinsa kuma yana samun sauki bayan da ya yanki jiki ya fadi kafin wasan sada zumunta tsakanin Real Madrid da AC Milan a California ranar Lahadi.

    Dan shekaru 54 yana aiki ne a matsayin manazarci ga gidan talabijin din Amurka ESPN. Ya yanki jiki ya fadi kasa yayin da ya ke gudanar da hira a filin wasa kafin wasan da aka buga a filin a Rose Bowl da ke Pasadena. Dan Thomas, wanda ke gabatarwa tare da Hislop, ya yi kira da a taimaka yayin da tashar ta yanke yada wasan na wucin gadi

    An ba da rahoton cewa yanayin zafi a California a ranar Lahadi ya kai 30C, amma ba a sani ba ko zafi ne ya haddasa sumar Hislop.

  4. Sadio Mane na nazarin tayin da Al-Nassr ta yi masa

    Dan wasan gaba na Bayern Munich Sadio Mane yana tunanin tayin komawa kungiyar Al-Nassr ta Saudi Arabiya.

    Mane, mai shekaru 31, bai sami yadda ya ke so a gasar Bundesliga ba bayan rashin samun nasara a kakar wasan farko bayan da ya bar Liverpool kan fan miliyan 35 a bara.

    Rahotanni sun nuna cewa Bayern a shirye take ta siyar da dan wasan dan kasar Senegal, inda kocin kungiyar Thomas Tuchel ya ce Mane ya gaza cimma burinsa.

    Mane ya tattauna da Al-Nassr amma babu wata yarjejeniya da kungiyar ta Saudiyya. Idan Mane ya koma kungiyar, zai hade da tsohon dan wasan gaban Manchester United Cristiano Ronaldo, yayin da Alex Telles da dan kasar Croatia Marcelo Brozovic suka koma kungiyar a bazara.

    Bayan nasarar da ya yi a Anfield inda ya lashe gasar zakarun Turai da gasar Premier, Mane ya koma Jamus a bazarar da ta gabata.

    Sai dai bai sami yadda ya ke so a kungiyar ba bayan rahotanni sun bullo cewa da ya kirbawa abokin wasansa Leroy Sane naushi bayan da Manchester City ta doke su a gasar zakarun Turai a watan Afrilu wanda hakan ya yi sanadiyan cire shi daga cikin tawagar tare da ci tararsa.

    • Mane da Sane sun bai wa hammata iska bayan wasan Man City
    • Senegal za ta dauko malamin tsubbu don yi wa Mane magani
  5. Tsohon dan wasan Ingila Trevor Francis ya mutu

    Tsohon dan wasan Ingila Trevor Francis ya rasu yana da shekaru 69 bayan ya yi fama da bugun zuciya a kasar Sifaniya.

    A shekara ta 1979 ya zama dan wasan kwallon kafa na farko na Biritaniya da aka siya kan fam miliyan daya bayan ya kammala canja kungiyar wasa daga Birmingham City zuwa Nottingham Forest.

    Ya lashe gasar cin kofin Turai guda biyu tare da Forest - a 1979, inda ya ci Malmo a wasan karshe, da kuma 1980.

    Francis ya kuma bugawa Ingila wasanni 52, inda ya ci kwallaye 12 kafin ya fara aikin horar da ‘yan wasan.

    Wata sanarwa da aka fitar a madadin iyalansa ta ce: "Wannan ya zo wa kowa da kowa a matsayin abin mamaki, duk mun shiga cikin matukar damuwa.

  6. Dortmund na shirin daukar Sabitzer daga Bayern

    Rahotanni sun bayyana cewa Borussia Dortmund na dab da kammala siyan dan wasan tsakiya Marcel Sabitzer daga Bayern Munich.

    Sky Sports Jamus ta ruwaito cewa kungiyoyin biyu sun amince da yarjejeniyar kusan Yuro miliyan 19, wanda ya hada da tsarabe-tsarabe.

    An shirya dan wasan na kasar Austriya zai yi gwajin lafiya kafin ya shiga tawagar BVB don yawon buga wasannin atisaye a Amurka.

    Dan wasan mai shekaru 29 ya nuna sha'awar buga gasar Premier ta Ingila bayan zaman aro a Manchester United a kakar wasan da ta wuce, amma da alama cewa Dortmund sun kulla yarjejeniya da Bayern.

    Idan cinikin ya tabbata, Sabitzer ne zai kasance dan wasa na biyu da Dortmund ta siya a bazara, bayan zuwan Felix Nmecha daga VfL Wolfsburg a farkon watan Yuli.

  7. Gasar cin kofin duniya: Brazil ta lallasa Panama

    Ary Borges ne ta zura zama wacce ta fara zura kwallo uku a wasa daya a gasar cin kofin duniya ta mata ta Fifa ta 2023 a lokacin da Brazil ta yi nasara akan Panama 4-0.

    'Yar wasan ta jefa kwallaye a farkon wasan kafin ta taimakawa ya kafa Bia Zanertto ta ci na uku jim kadan bayan haka, kafin ta ci wa Brazil ta hudu.

    Hakan na nufin Brazil ta ci gaba da rike tarihinta na lashe dukkanin wasanninta na farko guda tara a gasar cin kofin duniya ta mata.

    Tawagar Brazil ne kan gaba a rukunin F, bayan an yi canjaras a wasa tsakanin Faransa da Jamaica.

  8. Mamallakin Tottenham ya ba da umarnin sayar da Kane

    Mai kungiyar Tottenham Hotspur Joe Lewis ya shaidawa shugaban kungiyar Daniel Levy cewa dole ne a sayar da Harry Kane a bazara idan dan wasan ya ki sanya hannu kan sabon kwantaragi.

    Lewis ya kuduri aniyar ba za a bar Kane ya ga kai karshen kwantiraginsa na yanzu kuma ya tafi kyauta idan ya kare a bazara mai zuwa.

    Levy dai yana daraja Kane akan kudi fam miliyan 100 amma zai fuskanci matsin lamba ya siyar da kyaftin din na Ingila kafin karshen wa'adin sayan 'yan wasa idan ya ki amincewa da sabuwar kwantaragin da kungiyar ta shirya masa, wanda ake ganin zai kai fam 400,000 a mako.

    Tuni dai Tottenham ta yi watsi da tayi biyu da Bayern Munich ta yi kan Kane kuma yanzu tana shirin tayi na uku. Zakarun na Jamus suna da kwarin gwiwa cewa za a iya yin yarjejeniya, kuma an sami rahotannin cewa matar Kane Kate har ta fara neman gida a birnin Munich.

  9. Al Hilal ta Saudiyya ta taya Mbappe kan fan miliyan 259

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al Hilal ta Saudiyya ta gabatar da tayi mafi gwaɓi a tarihi na fan miliyan 259 a kan ɗan wasan PSG, Kylian Mbappe, kamar yadda kafar Press Association ta ruwaito.

    Ɗan wasan mai shekara 24, wanda ke da sauran kaka ɗaya a kwantaraginsa da PSG ya ƙi sanya hannu kan sabon kwantaragi, kuma ba ya cikin tawagar ƙungiyar da za ta buga wasannin sada zumunta gabanin fara kaka mai shigowa.

    PSG na son ta sayar da Mbappe a yanzu a maimakon barin sa ya tafi a kyauta a baɗi.

    Tafiyar ɗan wasa Neymar daga Barcelona zuwa PSG kan kuɗi fan miliyan 200 ita ce cinikin ɗan wasa mafi tsada a tarihi ya zuwa yanzu.

  10. Zaha na gab da komawa Galatasary

    Bayanai kan tafiyar Wilfred Zaha zuwa Galatasary na cewa ɗan wasan ya isa Turkiyya a daren da ya gabata yayin da ake gab da kammala cimma yarjejeniya.

  11. Barka da warhaka

    Yau ma za mu ci gaba da kawo muku yadda abubuwa ke wakana a kasuwar musayar ƴan wasa.