Boga na shirin komawa OGC Nice

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gefe na Atalanta Jeremie Boga yana gab da komawa kungiyar OGC Nice ta Faransa akan kusan Yuro miliyan 20.
A cewar majiyoyi daban-daban yarjejeniyar tana mataki na karshe kuma ana kan tattaunawa tsakanin kungiyoyin biyu.
Ana sa ran gabaɗayan farashin cinikin zai kai kusan Yuro miliyan 20. Wannan yana kusa da €22m da aka biya don siyan shi daga Sassuolo a 2022.
Boga ya kasance tsohon dan wasan bangaren matasa na Chelsea, ya tafi aro a Renne da Granada da Birmingham kafin a sayar da shi kan farashin €10m ga Sassuolo a 2018.
Yanzu yana da shekaru 26 kuma ya bugawa Ivory Coast wasanni 12 , inda ya zura kwallo daya a raga.











