''Har yanzu Maguire yana da mahimmaci a Man United''

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan muka kawo karshen shirin na labarin wasannin kai tsaye.

    Tareda fatan za ku tara ranar Litinin- Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper ke ce muku sai anjimanku

  2. ''Har yanzu Maguire yana da mahimmaci a Man United''

    Kociyan Manchester United, Erik ten Hag ya ce mai tsaron baya, Harry Maguire har yanzu ''dan wasa ne mai mahimmaci a kungiyar, duk da cewar ya karbe mukamin kfatin daga wajensa.''

    Ten Hag ya ce ya amince da bai wa Bruno Fernandez kan kwazon da yake sawa da rawar da yake takawa a United.

    Ole Gunnar ne ya bai wa Maguire kyallen kyaftin yake daurawa, wata uku da United ta sayo shi mai tsaron baya mafi tsada daga Leicester City.

    West Ham United ce ke son daukar Maguire, dan wasan tawagar Ingila.

    Maguire Ten Hag

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Daga jaridu

    Liverpool na tattaunawa da kungiyar Preston North End domin sayen matashin dan gabanta Layton Stewart, dan Ingila mai shekara 20. (Liverpool Echo)

  4. Wanda yake na daya a kwallon tennis a duniya, Carlos Alcaraz ya koma wasa bayan da ya lashe Wimbledon Open, amma ya sha kashi da ci 4-6 6-4 (10-8) a hannun David Goffin a Hopman Cup ranar Juma'a. Kenan Sifaniya ta yi rashin nasara a hannun Belgium da cin 2-1.

    Tennis

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Fulham ta kusan kammala daukar Salisu da Bassey

    Fulham ta kusan kammala cimma yarjejeniya da Southampton, domin sayen Mohammed Salisu. Ana cewa kudin cinikin ya kai fam miliyan 15.

    Monaco ma na sson sayen dan kwallon

    Haka kuma Fulham na daf da sayen mai tsaron bayan Ajax, Calvin Bassey kan kudi da zai kai Yuro miliyan 21.

    Calvin Bassey

    Asalin hoton, SNS

  6. Hearts ta dauki dan kwallon tawagar Australia, Nieuwenhof

    Herats ta sanar da kulla yarjejeniyar sayen dan wasan tawagar Australia, Calem, Nieuwenhof - abin da ya rage auna koshin lafiyarsa.

    Mai shekara 22 ya amince da kunshin yarjejeniyar kaka hudu, amma ba a fayyace kudin cinikin ba.

    Calem, Nieuwenhof

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Southampton ta yi wa Tino Livramento farashin fam miliyan 40

    Southampton ta yi wa Tino Livramento farashin fam miliyan 40, wanda tace tana fatan rike dan wasan domin ya buga mata Championship a kakar da za a fara cikin watan Agusta.

    Kungiyoyi da yawa na son daukar dan wasan ciki har da Newcastle United.

    Tun farko Newcastle ta taya dan wasan fam miliyan 30, amma Southampton ba ta sayar ba.

    Tino Livramento

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Atalantan na son daukar Rasmus, Daga Jaridu

    Atalanta ba ta da niyyar sassautowa a kan farashin fam miliyan 86 da ta sanya wa dan wasanta na gaba na Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 20, wanda Manchester United ke matukar so.(Mail)

  9. Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. Watakila Caicedo ya ci gaba da taka leda a Brighton

    Kociyan Brighton, Roberto de Zerbi ya ce yana tsara yadda zai yi aiki tare da Moises Caicedo cikin 'yan wasan da za su buga wa kungiyar tamaula a kakar 2023/24, duk da cewar Chelsea na son sayen dan wasan.

    Chelsea ta dade tana son daukar Caicedo, wadda ta yi ta yi fam miliyan 70, amma Brighton ba ta sayar mata da shi ba.

    Ana alakanta kungiyoyi da yawa da ke son sayen dan wasan mai shekara 21 dan kasar Ecuador, ciki har da Arsenal.

    Brighton

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Japan ta caskara Zambia 5-0 a gasar kofin duniya ta mata

    A gasar cin kofin duniya ta mata da ake yi a Australia da New Zealand, rukuni na hudu Denmark ta ci China 1-0.

    Karon farko da Denmark ta koma buga gasar cin kofin duniya tun bayan shekara 16.

    A rukuni na uku kuwa Japan ce ta caskara Zambia 5-0, yayin da Amurka mai rike da kofin ta doke Vietnam 3-0, ita kuwa Ingila ta yi nasara a kan Haiti da ci 1-0.

    Japan

    Asalin hoton, Getty Images

  12. Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. Werder Breman na rarrashin Fullkrug ya ci gaba da zama a kungiyar

    Werder Bremen tana ta rarrasin Niclas Füllkrug, domin ya ci gaba da taka leda a kungiyar.

    Bremen ta dauki dan wasan mai cin kwallaye a 2019, wanda ya yi ta fama da yin jinya.

    Füllkrug yana da sauran yarjejeniyar da za ta kare a Bremen zuwa karshen Yunin 2025, bayan da wasu kungiyoyin Turai da yawa ke son daukar dan wasan tawagar Jamus.

    Wasu da ke zawarcin dan wasan sun hada da Bayer Leverkusen da kuma Fiorentina.

    Niclas Füllkrug

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Ingila ta ci Haiti da kyar da gumin goshi a kwallon kafar mata

    Tawagar kwallon kafa ta mata ta Ingila ta ci ta Haiti 1-0 a wasan farko a rukuni da suka buga a gasar kofin duniya da suka kara a Brisbane.

    Wannan shine karon farko da Haiti ta fara buga gasar kofin duniya.

    England

    Asalin hoton, Getty Images

  16. Jakub Blaszczykowski ya sanar da yin ritaya

    Tsohon dan kwallon Borussia Dortmund, Jakub Blaszczykowski, wanda ya ci wa Poland kwallo 29 a wasa 109 ya sanar da yin ritaya.

    Wanda ya fara taka leda a Wisla Krakow, ya koma Borussia a 2007, wadda ya yi wa kaka 10 da yin kaka daya aro a Fiorentina.

    Ya koma Wolfsburg a 2016, wadda ya yi wa kaka uku daga nan ya sake komawa Wisla.Blaszczykowski ya ci kwwallo 28 a wasa 235 a gasar Bundesliga.

    Jakub Blaszczykowski

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Samuel Umtiti ya koma Lille daga Barcelona

    Mai tsaron bayan tawagar Faransa, Samuel Umtiti ya koma Lille, bayan da Barcelona ta amince ya bar kungiyar.

    Mai shekara 29, wanda ya buga wa Lyon tamaula kafin ya koma Barcelona, ya saka hannu kan kunshin yarjejeniyar kaka biyu da kungiyar da ke buga Ligue 1.

    Samuel Umtiti

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Messi ya fara cin kwallo a wasan farko a Inter Miami

    Kyaftin din Argentina, Lionel Messi ya ci kwallo a wasan farko da ya buga wa Inter Miami a bugun tazara.

    Tsohon dan kwallon Barcelona ya koma Inter Miami mi buga gasar kwallon kafar Amurka, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Paris St Germain a kakar da ta wuce.

    lIONEL mESSI

    Asalin hoton, Getty Images

  19. Jama'a barkanmu da kasancewa a shirin labaran wasanni kai tsaye daga BBC Hausa.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw zan gabatar muku da shirin.

    Za ku iya bayar da gudunmuwa kai tsaye a BBC Hausa Facebook.