AC Milan na zawarcin Okafor

Asalin hoton, NOAH.ARINZE/INSTAGRAM
AC Milan na daf da kulla yarjejeniya da Red Bull Salzburg kan Noah Okafor daga Salzburg, a cewar wani rahoto.
An sami labarin cewa Milan na gab da kulla yarjejeniya da Salzburg don siyan Okafor, kuma har kungiyar ta shirya gwajin lafiya da za a gudanar ranar Asabar a lokacin lokacin da dan wasan zai sauka a Milan, idan komai ya tafi yadda ya kamata.
An dade da tabbatar da cewa dan wasan kasar Switzerland ya riga ya amince yarjejeniya tsakaninsa da Rossoneri kuma yana cikin jerin sunayen Stefano Pioli na wadanda za su bugawa kungiyar a kaka mai zuwa, in ji dan jaridar.
Dan wasan mai shekaru 23, ya buga wa Salzburg wasanni 110, inda ya zura kwallaye 34 a raga kuma ya taimaka aka zura kwallaye 23 a wannan lokacin.
Ya zura kwallo a ragar Milan a gasar cin kofin zakarun Turai da aka buga a bara a Salzburg, wanda ya ba ta damar ci 1-0.
Ya buga mafi yawan wasanni a matsayin dan wasan gaba. Ya buga wasanni 60 a matsayin dan wasan gaba, inda ya zura kwallaye 23 sannan ya taimaka sau 15.













