Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ana alakanta Osinhen da cewar zai bar Napoli zuwa Man United

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan muka kawo karshe shirin.

    Da fatan za ku tara ranar Juma'a domin kawo muku wani labarin wasanni kai tsaye daga BBC Hausa.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw ke yi muku fatan alheri.

  2. Henderson ba zai buga wasan da Liverpool za ta kara da Karlsruher ba

    Kyaftin din Liverpool, Jordan Henderson ba zai buga wa kungiyar wasan sada zumunta da za ta kara da Karlsruher SC ba, bayan da ake ta batu kan makomarsa a Anfield.

    Ana alakanta shi da zai koma Al Ettifaq, kungiyar da ke buga gasar Saudi Arabia, wadda Steven Gerrard ke horarwa.

  3. Eddie Howe ya yaba kan kwazon Newcastle a wasa da Rangers

    Eddie Howe ya kwatanta wasan da Newcastle United ta ci Rangers 2-1 ranar Talata da cewar tamkar gasar zakarun Turai suka buga, saboda ingancin karawar a filin wasa na Ibrox.

    Miguel Almiron da Harrison Ashby ne suka ci wa Newcastle kwallaye.

  4. Wasannin da Najeriya za ta buga a gasar kofin duniya

  5. Liverpool ba za ta sayar da Luis Diaz ba

    Liverpool ba ta da shirin sayar da Luis Diaz, kamar yadda The Athletic ta wallafa.

    Dan kasar Colombia ya koma Anfield da taka leda daga Porto a Janairun 2022, wanda yanzu ake alakanta shi da Al Hilal kan fam miliyan 43.3, kudin da ake ganin Liverpool za ta amince da tayin.

    Tuni Liverpool ta bai wa dan kwallon riga mai lamba bakwai, wadda take fatan zai taka rawar gani a kakar 2023/24, wanda ya yi fama da jinya a kakar da ta wuce.

    Diaz shine na uku daga Liverpool da ake alakanta su da komawa buga gasar Saudi Arabia, bayan Fabinho da kuma Jordan Henderson.

  6. Al Ahli ta dauki Mahrez daga Man City

    Manchester City ta amince ta sayar da Riyad Mahrez kan fam miliyan 30 ga Al-Ahli.

    Mai shekara 32 an bashi izinin da kada ya bi City wasannin sada zumunta da za ta buga a Japan da kuma Koriya ta Kudu.

    Tuni dai City ta amince da tayin da aka yi wa dan kwallon Algeria, wanda darajar dan kwallon ta yi daidai da shi, wanda saura kaka biyu yarjejeniyarsa ta kara a Etihad.

  7. Mason Mount ya buga wa United wasan da ta ci Lyon 1-0

  8. Rooney na fatan Rashford zai kara nuna kansa a duniya

    Wayne Rooney ya ce shekara biyar mai zuwa ita ce da Marcus Rashford ya kamata ya nuna kansa a fagen taka leda a duniya tare da Mancheste United.

    A makon nan Rashford ya saka hannu kan kwantiragin da zai ciga da taka leda a Old Trafford har zuwa karshen kakar 2028.

  9. Wasu cinikin 'yan wasa da aka yi ranar Laraba a Premier League

    Zeki Amdouni[Daga Basel zuwa Burnley]

    Benie Traore[Daga Hacken zuwa Sheffield United]

    English Football League

    Ethan Ampadu[Daga Chelsea zuwwa Leeds] kan fam miliyan bakwai

    James Balagizi[Daga Liverpool zuwa Wigan] Wasannin aro zai buga

    Abu Kamara[Norwich - Portsmouth] Wasannin aro zai buga

    Viljami Sinisalo[Aston Villa - Exeter] Wasannin aro zai buga

    Joseph Hungbo[Daga Watford zuwa FC Nurnberg]

    Wasu cinikin da bai shafi Premier League ba

    Benjamin Mendy[ Zuwa Lorient]

    Oriol Romeu[Daga Girona zuwa Barcelona]

  10. Ko yaya makomar Saint-Maximin a Newcastle?

    Eddie Howe ya yi magana kan makomar Allan Saint-Maximin a Newcastle, wanda bai yi wa kungiyar wasan sada zumunta da ta ci Rangers 2-1 ba ranar Talata, wanda aka ce da kyar idan zai je Amurka wasannin da za ta buga.

  11. Za a yi sha'awar kallon wasannin kwallon kafar mata - Infantino

    Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infantino ya ce wasan tamaular mata na samun cin gaba tun daga shekara goma da ta wuce.

    Ya kuma ce yana da kwarin gwiwa cewar masu sukar wasannin za su yi matukar son gasar kwallon kafa ta mata nan gaba.

    Fifa na sa ran mutum biliyan biyu ne za su kalli gasar kofin duniya ta mata da za a fara a ranar Alhamis a Aucland da za a yi fafatawa 64 da Australia da New Zealand za su karbi bakunci.

    Kasashe hudu ne daga Afirka da za su wakilce ta da suka hada da Morocco da Zambia da Nigeria da Afirka ta Kudu mai tawagar da ake kira Banyana Banyana.

  12. Labarai da dumi-dumi, Man United ta ci Lyon 1-0 a wasan sada zumunta

    Manchester United ta doke Lyon 1-0 a wasan sada zumunta, kuma Donny van de Beek ne ya ci mata kwallon bayan da suka koma zagaye na biyu a karawar.

    United za ta ziyarci Amurka domin buga wasan sada zumunta da Arsenal.

  13. Tonali ya fara wasa a Newcastle da kafar dama

    Eddie Howe ya sanar cewar sabon dan wasan da ya dauka Sandro Tonali ya taka rawar gani a wasan sada zumunta da Newcastle ta ci Rangers 2-1 ranar Talata.

    Newcastle ta dauki dan kwallon kan fam miliyan 55, wanda ya buga minti 45 a karawar da suka yi a filin wasa da ake kira Ibrox.

  14. Man United ta samu Onana madadin David de Gea

    Tuni David de Gea ya hakura da Manchester United, bayan kaka 12 a kungiyar da taka leda karo 545 tun lokacin da ya koma Old Trafford karkashin Sir, Alex Ferguson.

    Mai tsaron ragar ya yi wasa 190 ba tare da kwallo ya shiga ragarsa ba

    Onana ya yi kaka bakwai da rabi a Ajax daga nan ya koma Inter Milan a Yulin 2022, bayan da kwantiraginsa ya kare.

  15. RB Leipzig ta dauki El Chadaille Bitshiabu daga PSG

    RB Leipzig ta dauki matashin dan wasa El Chadaille Bitshiabu daga Paris Saint-Germain, kamar yadda kungiyar da ke buga Bundesliga ta sanar.

    Leipzig ta ce dan wasan mai shekarar 18, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar, wadda za ta kare a karshen kakar 2028.

    Bitshiabu ya fara yi wa PSG tamaula yana da shekara 19, wanda ke buga wa tawagar Faransa tamaula ta matasa 'yan kasa da shekara 19.