Nan muka kawo karshen shirin
Da fatan za ku tara ranar Laraba domin kawo muku labarin wasannin kai tsaye.
Sunana Mohammed Abdu nake muku fatan alheri.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.
Mohammed Abdu
Da fatan za ku tara ranar Laraba domin kawo muku labarin wasannin kai tsaye.
Sunana Mohammed Abdu nake muku fatan alheri.
Kim Min-jae ya bar Napoli, wadda ta lashe Serie A, kamar yadda dan kwallon tawagar Koriya ta Kudu ya sanar ranar Talata, wanda ake alakanta shi da zai koma Bayern Munich.
Mai tsaron baya, mai shekara 26 ya koma Napoli daga Fernabahce a Yulin bara.
Dan kwallon ya taka rawar gani da Napoli ta lashe kofin Serie A kuma a karon farko bayan shekara 30.
Shine aka bayyana a matakin fitatcen mai tsaron baya a Serie A da ta wuce.
Rory Mcllroy ya ce lashe Scottish Open a kwallon golf da ya yi a karshen mako alama ce ta zai taka rawar gani a makon nan a gasar Open Championship da za a yi a Royal Liverpool.
Babban kofi a kwallon golf da ya lashe shine a 2014 a Royal Liverpool, wanda ke fatan kawo karshen kaka tara ba tare da daukar PGA Tour ba.

Asalin hoton, Getty Images
Sabon kociyan Tottenham, Ange Postecoglou ya fara jan ragamarr kungiyar da kafar hagu, bayan da ya yi rashin nasara a wasan sada zumunta da ci 3-2 a hannun West Ham United.

Asalin hoton, Getty Images
Ranar 20 ga watan Yli za a fara gasar cin kofin duniya ta mata da Australia da New Zealand za su karbi bakuncin wasannin.
Afirka za ta samu wakilci Morocco da Zambia da za su guda gasar a karon farko, sauran sun hada da Afirka ta Kudu da Najeriya.

Asalin hoton, BBC Sport
Akwai rahotanni da dama da yake batun kan wanda zai maye gurbin Fabinho, koda dan kwallon Liverpool zai koma Saudi Arabia da taka leda a Al Ittihad.
Ana cewa watakila kungiyar Anfield ta sayo dan wasan Manchester City and Kalvin Phillips, wasu labaran na cewa watakila ta dauki dan wasan Crystal Palace, Cheick Doucoure.
Tuni dai Al Ittihad ta yi tayin fam miliyan 40, wanda kudi ne mai kyau da Liverpool za ta iya karba.

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron bayan Chelsea, Wesley Fofana za iyi jinya, bayan da likitoci za su yi masa aiki kan raunin da ya ji.
Mai shekara 24 bai bi kungiyar wasan atisaye da ta je Amurka, don tunkarar kakar 2023/24.
Chelsea ta kare a mataki na 12 a gasar Premier League da ta wuce.

Asalin hoton, BBC Sport
Filin wasa na Hampden Park na kokarin karbar bakuncin gasar zakarun Turai ta 2026 ko kuma ta 2027.
Hukumar kwallon kafar Scotland na fatan shirya gasar mata ta Champions League da ta Europa League da kuma Conference League, wadda ke fatan mika takardun neman izini nan da 21 ga watan Fabrairun 2024.
Yuwefa tace babban kwamitinta zai fayyace filayen da za su karbi bakuncin wasa karshe takwas a kwallon maza da ta mata a Mayun 2024.
Katafaren filin wasa da ke Glasgoww ya taba karbar wasan karshe shida a gasar zakarun Turai.
Kasashe tara ne ke son karbar bakuncin wasan karshe, yayin da filin Milan da na Budapest ke son klarbar wasan karshe a Champions League na maza.
Masu neman karbar bakuncin wasan karshe a gasar zakarun Turai
Wasan karshe Champions League karawar maza
Champions League final wasannin mata
Wasan karshe a Europa League
Wasan karshe a Europa Conference League final

Asalin hoton, Getty Images
Sky Sports ta ce shugaban kungiyar Paris St Germain, Nasser Al-Khelaifi zai gana da dan kwallon tawagar Faransa, Kylian Mbappe a karon farko, bayan da mai shekara 24 ya rubuta wasikar cewar ba zai tsawaita yarjejeniyarsa a kungiyar da zarar an kammala kakar da za a fara a cikin watan Agusta.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Kociyan tawagar Ingila, Gareth Southgate ya bukaci Harry Maguire yake buga wasanni a koda yauce, ko kuwa ba zai je da shi gasar kofin nahiyar Turai da za a buga a 2024 a Jamus ba.
A 2019 Manchester United ta sayo Maguire daga Leicester City a matakin mai tsaron baya mafi tsada a duniya.
Wata uku tsakani Ole Gunnar Solskjaer ya fara bashi kyallen kyaftin din United yake daurawa daga baya aka tabbatar masa da mukamin bayan da Ashley Young ya koma Inter Milan da taka leda.
Tuni dai Maguire ya sanar da cewar an karbe mukamin kyaftin daga wajensa, tuni kuma Erik ten Hag ke amfani da masu tsaron baya da suka hada da Raphael Varane da Lisandro Martinez da Victor Lindelof da kuma Luke Shaw.
Yanzu dai ana cewa West Ham United ce ke son daukar Maguire.

Asalin hoton, Getty
An wanke tsohon dan wasan tawagar Wales da Manchester United, Ryan Giggs kan zargin cin zarafin budurwarsa da kanwarta.
Wata kotu ce a Manchester ta soke dukkan tuhume - tuhumen da aka yi masa. Giggs mai shekara 48, ya dade yana musanta zargin cin zarafin Kate Greville mai shekara 38 da kuma kanwarta Emma.
Mai shari'a Hillary Manley ce ta wanke Giggs daga dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.

Asalin hoton, Getty Images
Cristiano Ronaldo ya ce ba zai sake komawa nahiyar Turai buga tamaula ba, ya kuma kara da cewar gasar kwallon kafar Saudi Arabia ta dara ta Amurka daraja nesa ba kusa ba..
Lionel Messi ya koma taka leda a Inter Milami mai buga gasar Amurka, bayan da yarjejeniyarsa ta kare a Paris St Germain a karshen kakar 2022/23.
Ronaldo, tsohon dan wasan Real Madrid da Juventus ya koma Al Nassr cikin watan Disamba kan kwantiragin kaka biyu da rabi daga Manchester United.
Dan kwallon tawagar Portugal ya ce ya buge hanyar da fitattun 'yan kwallo ke komawa buga gasar Saudi Arabia - yana sa ran 'yan wasa da dama nan gaba za su koma can da taka leda.

Asalin hoton, Reuters
Dan wasan Arsenal, Folarin Balogun na son sanin makomarsa a Emirates a shirin tunkarar kakar bana.
Mai shekara 22 ya buga wasannin aro a Reims a bara, wanda shine na hudu a yawan ci wa kungiyar kwallaye.
Balogun ya ce kwallo 21 da ya zura a raga ya kara samun kwarewa a kololuwar tamaula.
Inter Milan na son daukar dan wasan tawagar Amurka, amma har yanzu Arteta bai yanke shawarar ko zai bar Balogun ya bar Arsenal ba.

Asalin hoton, Getty Images
The Athletic ta wallafa sabon labarin cewar Manchester United ta amince da tayin £43.9m da karin tsarabe-tsarabe kan sayen mai tsaron ragar Inter Milan, Andre Onana.
Ana sa ran sanar da kammala cinikin a kowanne lokaci, bayan da kungiyoyin biyu ke daf da kammala kulla yarjejeniya.
United za ta je Amurka daga Scotland buga wasannin atisayen tunkarar kaka mai zuwa, bayan ta kara da Lyon a Edinburgh ranar Laraba.

Asalin hoton, Getty Images
Kociyan Arsenel Mikel Arteta ya ce yana cike da farin ciki kan cefanen da kungiyar ke yi kan fara kakar nan, watakila ya kara sayo dan wasa nan gaba.
Tuni dai Gunnar ta kammala daukar Declan Rice daga West Ham ranar Asabar, bayan daukar Kai Havert da Jurien Timber.
Arsenal za ta buga wasan sada zumunta ranar Laraba a Amurka da MLS All Stars - yayin da Gunners za ta fara Premier League a Emirates da Nottingham Forest ranar 12 ga watan Agusta.

Asalin hoton, PA Media
Watakila ranar Talata Manchester United ta sanar da tsawaita zaman Marcus Rashford a kungiyar kan yarjejeniyar kaka biyar da za ta kare zuwa karshen 2028.
Mai shekara 25 ya fara taka leda a kungiyar Old Trafford tun daga matasanta - wanda yanzu ya ci kwallo 123 a wasa 359.
Rashford, wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar da za a fara - ya ci kwallo 30 a karon farko a kakar tamaula ta 2022/23.
A dai United din ana cewar ta kusan kammala cinikin golan Kamaru, Andre Onana daga Inter Milan, wanda ya tsare raga karkashin Ten Hag a Ajax.

Asalin hoton, Getty Images
Jama'a barkanmu da wannan lokacin labarin wasanni kai tsaye tare da Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw.
Shafi ne da zai ke kawo muku irin labaran wasanni da ke gudana a rana irin ta Talata.
Za ku iya bayar da gudunmuwa kai tsaye ko BBC Hausa Facebook ko ta Instagram.