Yadda aka rufe kasuwar cinikayyar 'yan kwallo a Turai ta Janairu

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan muka kawo karshen shirin

    Da fatan za ku tara ranar Alhamis domin kawo muku wani shirin.

    Ga wasu jerin tambayoyi ga masu bibiyar wasanni:

    Shin ko Chelsea za ta koma kan ganiya bayan daukar Enzo Fernandez?

    Ko Graham Potter zai iya tsara fitattun da suka da ce a wasannin Chelsea.

    Daukar da Arsenal ta yi wa Jorginho ko zai lashe Premier League?

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tudun Wada ke muku fatan mu wuni lafiya.

  2. Chelsea ta sayar da Jorginho bayan daukar Fernandez, Arsenal

    Bayan da Chelsea ta tabbatar da cewar ta dauki Enzo Fernandez daga Benfica, hakn ya sa ta sayar da Jorginho ga Arsenal kan fam miliyan 12.

    Mai shekara 31 ya saka hannu kan yarjejeniyar wata 18 da amincewar za a iya kara tsawaita masa kaka daya idan ya yi kwazon da ake bukata

    Ya koma Chelsea daga Napoli a 2018, kuma saura wata shida kwantiraginsa ya kare a Chelsea.

    Jorginho

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Pedro Porro ya koma Tottenham buga wasannin aro, Tottenham

    Tottenham ta dauki aron mai tsaron baya Pedro Porro daga Sporting Lisbon domin buga mata wasannin aro zuwa karshen kakar bana.

    Haka kuma cikin kunshin yarjejeniyar za a iya sayar mata da shi fam miliyan 40.

    pedro

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Ramadan ya buge Karfe

    Ramadan ya buge Karfe a damben gargajiya da aka buga ranar Talata a gidan wasa da ke Ado Bayero Square a Kano Najeriya.

    Ramadan dan damben Arewa ya yi nasara ne a turmi na biyu a kan Karfe maci karafa dan wasan Kudu.

    Damben gargajiya
  5. Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. An yi mamaki da Gurdiola ya bar Cancelo zuwa Bayern Munich

    An yi mamaki da Manchester City ta bar mai tsaron bayanta Joao Cancelo ya koma buga wasannin aro zuwa Bayern Munich.

    Mai shekara 28 yana cikin 'yan kwallon da suka bai wa Pep Guardiola damar lashe Premier League biyu baya.

    Zai taka leda aro a Bayern da yarjejeniyar sayar da shi sama da fam miliyan 61 idan ya taka rawar gani.

    Joao Cancello

    Asalin hoton, BBC Sport

  7. Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Everton ba ta dauki dan kwallo ba, bayan daukar Dyche, Everton

    Kungiyar Everton wadda take ta karshe a teburin Premier League ba ta dauki dan kwallo ko daya ba, bayan da ta sanar da daukar sabon koci Sean Dyche ranar Litinin.

    A tsakar daren Talata aka kammala cinikayyar 'yan kwallo a Turai.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Cefanen 'yan kwallo mafi tsada da aka yi a Birtaniya

    Expensive British Transfer

    Asalin hoton, BBC Sport

  10. Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Za a yi wa Antonio Conte tiyata, Tottenham

    Tottenham ta sanar cewar za a yi wa kociyanta, Antonio Conte tiyata ranar Laraba.

    Mai shekara 53 ba zai ja ragamar wasan Premier League ba kenan da Manchester City da Pep Guardiola zai kai ziyara ranar Lahadi.

    Antonio Conte

    Asalin hoton, PA Media

  12. Wasu cinikin da ba a kammala ba a Janairu

    Ranar Talata 31 ga watan Janairu aka rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo a wasu kasashe a Turai.

    Duk da kudin da aka kashe masu yawa, ba kowa ya samu yadda yake bukata ba.

    An kasa cimma matsaya kan dan wasan Morocco Hakim Ziyech daga Chelsea zuwa Paris St Germain.

    Arsenal ba ta samu daukar dan kwallon Brifghton, Moises Caicedo, duk da ta yi na biyu kan fam miliyan 70.

    Conor Gallagher ya zabi ci gaba da taka leda a Stamford Bridge, duk da cewar Everton ta yi kokarin daukar dan kwallon.

    Duk da cewar Everton ta dauki Sean Dyche ranar Litinin a matakin sabon kociyanta, sai dai kungiyar ba ta dauki dan kwallo ba har aka rufe kasuwar cinikin 'yan wasa ranar Talata.

    Moises Caicedo

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Wasannin mako na biyar a Firimiyar Najeriya

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. Wasu siyayyar da aka yi a ranar rufe kasuwa

    20:03 Jorginho [Chelsea - Arsenal] £12m

    21:00 Naouirou Ahamada [Stuttgart - Crystal Palace] £9.7m

    22:16 Albert Sambi Lokonga [Arsenal - Crystal Palace] Loan

    22:57 Pedro Porro [Sporting Lisbon - Tottenham] aro za a iya sayar da shi £40m

    23:40 Harry Souttar [Stoke - Leicester] £15m zai kai £20m da karin tsarabe tsarabe

    Done Deal

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Labarai da dumi-dumi, Chelsea ta dauki Fernandez a matakin mafi tsada a Birtaniya

    Chelsea ta kammala daukar dan kwallon Argentina, Enzo Fernandez daga Benfica kan fam miliyan 107 a matakin mafi tsada da aka saya a Birtaniya.

    Kudin cinikayyar ya haura fam miliyan 100 da Manchester City ta dauki Jack Grealish a 2021.

    Fernandez, wanda ya koma Benfica kan fam miliyan 10 a cikin watan Agusta, shi ne matashin dan kwallon mafi kwazo a gasar kofin duniya da aka yi a Qatar.

    Enzo Fernandez

    Asalin hoton, Getty Images

  16. Wembley ta bambanta da lokacin da Newcastle ta yi wasan karshe a 1999, Newcastle 2-1 Southampton (Agg: 3-1)

    Filin wasa na Wembley ya sauya matuka tun bayan da Newcastle United ta buga wasan karshe a FA Cup a 1999, inda ta yi rashin nasara da ci 2-0 a hannun Manchester United

    A kakar ce kungiyar Old Trafford ta lashe kofi uku jumulla.

    Newcastle

    Asalin hoton, Getty Images

    Newcastle

    Asalin hoton, Getty Images

    Newcastle

    Asalin hoton, Getty Images

    Newcastle

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Tsohon dan wasan Newcastle, Lee Clark ya ce tun bayan da kungiyarsu ta doke Leicester City a Carabao Cup zagayen quarter-final, wasu magoya baya suka fara shirin zuwa Wembley domin buga wasan karhe.

    Yanzu za su kara a wasan karshe a Wembley a Carabao Cup ranar 26 ga watan Fabrairu a karon farko tun bayan 1999 a FA Cup.

    Now they know they'll definitely be at Wembley on 26 February - for the first time since reaching the FA Cup final in 1999.

    Carabao Cup

    Asalin hoton, Daily Mail

  18. Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Newcastle ta kai wasan karshe a karon farko tun 1999, Carabao Cup

    Newcastle United ta kai wasan karshe a karon farko tun bayan 1999, bayan da ta doke Southampton a Carabao Cup ranar Talata a St James' Park.

    Eddie Howe zai jira wadda za ta kai wasan karshe tsakanin Manchester United ko Nottingham Forest a Wembley.

    Rabon da Newcastle ta lashe wani babban kofi tun 1968, bayan da ta ci Inter Cities' Fairs Cup in 1969.

    Carabao Cup

    Asalin hoton, Reuters

  20. Jama'a barkanmu da wannan lokacin

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper zan gabatar muku da labarin wasanni kan tsaye.

    Za kuji yadda aka kammala cinikayyar 'yan kwallo a Turai a watan Janairu.

    Sai wasan Cabao Cup da aka buga ranar Talata da na Man United da Forest

    Da sauran batutuwan da suka shafi labarin wasanni.

    Za ku iya bayar da gudunmuwa a lokacin da muke gabatar da shirin a BBC Hausa.