Mun kawo karshen shirin
Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara a gobe Talata.
Ranar Talata za mu kawo muku wasu daga cefanen da ak yi a watan Janairun.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW ke fatan wuni lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.
Mohammed Abdu
Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara a gobe Talata.
Ranar Talata za mu kawo muku wasu daga cefanen da ak yi a watan Janairun.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW ke fatan wuni lafiya.
Tsohon dan wasan Burnley, Sam Vokes ya ce ba wani kociya da ya dace Everton ta dauka fiye da Sean Dyche.
Tuni dai kungiyar Goodison Park ta kori Frank Lampard.
The Mail ta wallafa cewar Inter Milan na son daukar Harry Maguire.
Daman yanzu dan kwallon baya buga wasanni sosai a Manchester United, saboda haka tafiyarsa ba za ta haifar da matsala ba.
Nottingham Forest za ta amince ta bayar da aron Lewis O’Brien zuwa karshen kakar bana.
Ana sa ran Janjo Shelvey zai koma taka leda a City Ground, saboda haka ne Steve Cooper is zai bayar da aron O’Brien, wanda ya koma Forest daga Forest Huddersfield a bana.
Ranar Lahadi a gidan wasa da ke Ado Bayero Square aka yi dambe da yawa, inda aka karrama Ramadan, wanda ya yi kisan dambe 79 a jihar Kano a 2022.
Hakan ya sa aka yi dambe domin karrama shi.
Wasannin da suka yi kisa:
Shagon Gwagwarwa daga Kudu ya gude Bahagon 'Yan sanda daga Arewa
Karfe daga Kudu ya yi nasara a kan Dan Bichi daga Arewa
Wasannin da ba kisan dambe:
Dan Aliyu da Bahagon Danladin Geza daga Guramada
Shagon Mada daga Kudu da Inda daga Arewa
Autan Sikido daga Kudu da Shagon Tuwo daga Arewa
Shagon Musan Kaduna daga Arewa da Shagon Habu Cingam daga Kudu
Sakamakon wasannin zagaye na hudu a FA Cup da aka buga ranar Lahadi
Dan kwallon Stuttgart, Naouirou Ahamada yana Selhurst Park ana auna koshin lafiyarsa a shirin komawa Crystal Palace da taka leda.
Ahamada ya taka leda a matasan kungiyar Juventus daga baya ya koma taka leda a Bundssliga.
Ya yi wa Stuttgard wasa 18 a dukkan karawa da cin kwallo biyu.
Wani dan jarida daga Italiya ya ce har yanzu Tottenham ba ta hakura da son daukar dan wasan Sporting Lisbon, mai tsaron baya Pedro Porro ba.
Kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya ce ba wani dan wasan da ta dauka, duk da cewar za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai ranar Talata.
Ya tabbatar da cewar a wannan lokacin ba wani dan wasan da zai bar Santiago Bernabeu ba kuma wanda za ta dauka.
Kociyan Brighton, Roberto de Zerbi ya ce ya yi farin ciki kan rawar da 'yan wasa suka taka da ta kai sun fitar da Liverpool daga FA Cup.
Ya kara da cewar ranar Lahadi ta su ce, suna alfahari da kwazon da suka yi da ta kai sun yi waje da mai rike da FA Cup a bana.
Brighton ta yi nasara da ci 2-1 a zagaye na hudu a FA Cup.
Jurgen Klopp ya mayar da martani ga masu sukarsa da cewar, ba haka kawai rana daya ya zama koci mara taka rawar gani ba.
Liverpool mai rike da FA Cup, wadda Brighton ta fitar da ita ranar Lahadi tana ta tara a Premier League da tazarar maki 10 tsakaninta da 'yan hudun farko a teburin babban gasar tamaula ta Ingila.
A bara saura wasa biyu a kakarkare kakar, amma tana takarar Carabao da FA da kuma Premier League.
Dan wasan Juventus, Weston McKennie ya sauka Landan da safiyar nan kan shirin komawa Leeds United da taka leda.
Ana sa ran zai buga wasannin aro zuwa karshen kakar bana, amma da zabin Leeds za mallake shi idan ya taka rawar gani.
Kungiyoyi da dama sun yi zawarcin dan wasan Amurka, amma ya zabi komawa Leeds United domin buga tamaula tare da takororinsa kamar Tyler Adams da kuma Brenden Aaronson.
Zai zama dan wasa na uku da Leeds ta dauka a Janairun nan, bayan Max Wober da Georginio Rutter.
The Sky ta bayar da rahoton cewar watakila Benfica ta sanar da Chelsea cewar ba za ta sayar mata da Enzo Fernandez ba, wanda take ta nacin sai ta dauka a Janairun nan.
Dan wasan tawagar Argentina yana da kunshin kwantiragin sama da fam miliyan 105, idan har kungiyar Stamford Bridge ta biya kudin zai zama mafi tsada a Premier League kenan.
Brighton ta ki sallama tayi na biyu da Arsenal ta yi wa dan kwallon tawagar Ecuador, Moises Caicedo ta kuma ce bana sayarwa ba ne.
An ce tayin ya kai fam miliyan 70.
The latest bid is thought to be in the region of £70m.
Arsenal da Chelsea na rububin daukar dan wasan mai shekara 21 kafin ranar talata a rufe kasuwar cinikayyar 'yan wasa ta Turai.
Sai dai bai buga wa Brighton FA Cup da ta doke Liverpool 2-1 ranar Litinin ba.
The Telegarph ta bayar da rahoton cewar Janjo Shelvey zai koma taka leda a Nottingham Forest, zai zama na 25 da za ta dauka tun bayan da ta koma buga Premier League a bana.
Jama'a barkanmu da kasancewa a cikin shirin labarin wasanni kai tsaye.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW zan gabatr muku da shirin.
Za ku iya bayar da gudunmuwa a lokacin da muke gabatar da shirin a BBC Hausa Facebook da kuma a Twitter.