Za a rufe kasuwar cinikayyar 'yan kwallo ranar Talata

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Mun kawo karshen shirin

    Nan muka kawo karshen shirin da fatan za ku tara a gobe Talata.

    Ranar Talata za mu kawo muku wasu daga cefanen da ak yi a watan Janairun.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW ke fatan wuni lafiya.

  2. Kwazon da Dyche ya yi a Premier League

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Har yanzu Everton ba ta sanar da daukar sabon koci ba, Everton

    Tsohon dan wasan Burnley, Sam Vokes ya ce ba wani kociya da ya dace Everton ta dauka fiye da Sean Dyche.

    Tuni dai kungiyar Goodison Park ta kori Frank Lampard.

    Sean Dyche

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Inter Milan na son sayen Harry Maguire

    The Mail ta wallafa cewar Inter Milan na son daukar Harry Maguire.

    Daman yanzu dan kwallon baya buga wasanni sosai a Manchester United, saboda haka tafiyarsa ba za ta haifar da matsala ba.

    Harry Maguire

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Nottingham Forest za ta bayar da aron O'Brien, Nottingham Forest

    Nottingham Forest za ta amince ta bayar da aron Lewis O’Brien zuwa karshen kakar bana.

    Ana sa ran Janjo Shelvey zai koma taka leda a City Ground, saboda haka ne Steve Cooper is zai bayar da aron O’Brien, wanda ya koma Forest daga Forest Huddersfield a bana.

    Lewis O’Brien

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Na Gwagwarwa ya buge Shagon 'Yan sanda, Damben gargajiya

    Ranar Lahadi a gidan wasa da ke Ado Bayero Square aka yi dambe da yawa, inda aka karrama Ramadan, wanda ya yi kisan dambe 79 a jihar Kano a 2022.

    Hakan ya sa aka yi dambe domin karrama shi.

    Wasannin da suka yi kisa:

    Shagon Gwagwarwa daga Kudu ya gude Bahagon 'Yan sanda daga Arewa

    Karfe daga Kudu ya yi nasara a kan Dan Bichi daga Arewa

    Wasannin da ba kisan dambe:

    Dan Aliyu da Bahagon Danladin Geza daga Guramada

    Shagon Mada daga Kudu da Inda daga Arewa

    Autan Sikido daga Kudu da Shagon Tuwo daga Arewa

    Shagon Musan Kaduna daga Arewa da Shagon Habu Cingam daga Kudu

    Damben gargajiya
  7. Sakamakon FA Cup na mata zagaye na hudu, FA Cup

    Sakamakon wasannin zagaye na hudu a FA Cup da aka buga ranar Lahadi

    • Tottenham 5-0 London City Lionesses
    • Everton 0-1 Birmingham City
    • Manchester City 7-0 Sheffield United
    • Sunderland 1-2 Manchester United
    • Chelsea 3-2 Liverpool
    • Wolverhampton 0-2 West Ham
    • Arsenal 9-0 Leeds
    • West Brom 0-7 Brighton
    • Leicester City 2-2 (2-3 on penalties) Reading
    • Aston Villa 11-0 Fylde
    Women FA Cup

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Ana auna koshin lafiyar Naouirou Ahamada a Palace, Crystal Palace

    Dan kwallon Stuttgart, Naouirou Ahamada yana Selhurst Park ana auna koshin lafiyarsa a shirin komawa Crystal Palace da taka leda.

    Ahamada ya taka leda a matasan kungiyar Juventus daga baya ya koma taka leda a Bundssliga.

    Ya yi wa Stuttgard wasa 18 a dukkan karawa da cin kwallo biyu.

    Naouirou Ahamada

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Har yanzu Tottenham na son daukar Porro

    Wani dan jarida daga Italiya ya ce har yanzu Tottenham ba ta hakura da son daukar dan wasan Sporting Lisbon, mai tsaron baya Pedro Porro ba.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. Ba dan wasan da Real Madrid za ta dauka a Janairu - Ancelotti, Real Madrid

    Kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya ce ba wani dan wasan da ta dauka, duk da cewar za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai ranar Talata.

    Ya tabbatar da cewar a wannan lokacin ba wani dan wasan da zai bar Santiago Bernabeu ba kuma wanda za ta dauka.

    Carlo Ancelotti

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. Chelsea ta fara tattaunawa kan dauko dan wasan Benfica, Enzo Fernández, Sakonnin da kuke aikewa a BBC Hausa Facebook

  14. Na yi murna da kuma cire Liverpool daga FA Cup - De Zerbi

    Kociyan Brighton, Roberto de Zerbi ya ce ya yi farin ciki kan rawar da 'yan wasa suka taka da ta kai sun fitar da Liverpool daga FA Cup.

    Ya kara da cewar ranar Lahadi ta su ce, suna alfahari da kwazon da suka yi da ta kai sun yi waje da mai rike da FA Cup a bana.

    Brighton ta yi nasara da ci 2-1 a zagaye na hudu a FA Cup.

    Roberto de Zerbi

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Klopp ya ce ba haka kawai ya zama koci mara kokari ba, Liverpool

    Jurgen Klopp ya mayar da martani ga masu sukarsa da cewar, ba haka kawai rana daya ya zama koci mara taka rawar gani ba.

    Liverpool mai rike da FA Cup, wadda Brighton ta fitar da ita ranar Lahadi tana ta tara a Premier League da tazarar maki 10 tsakaninta da 'yan hudun farko a teburin babban gasar tamaula ta Ingila.

    A bara saura wasa biyu a kakarkare kakar, amma tana takarar Carabao da FA da kuma Premier League.

    Jurgen Klopp

    Asalin hoton, Getty Images

  16. Weston MCKennie zai koma Leeds daga Juventus, Leeds United

    Dan wasan Juventus, Weston McKennie ya sauka Landan da safiyar nan kan shirin komawa Leeds United da taka leda.

    Ana sa ran zai buga wasannin aro zuwa karshen kakar bana, amma da zabin Leeds za mallake shi idan ya taka rawar gani.

    Kungiyoyi da dama sun yi zawarcin dan wasan Amurka, amma ya zabi komawa Leeds United domin buga tamaula tare da takororinsa kamar Tyler Adams da kuma Brenden Aaronson.

    Zai zama dan wasa na uku da Leeds ta dauka a Janairun nan, bayan Max Wober da Georginio Rutter.

    Weston McKennie

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Chelsea ta dage kan daukar Enzo Fernandez daga Benfica, Chelsea

    The Sky ta bayar da rahoton cewar watakila Benfica ta sanar da Chelsea cewar ba za ta sayar mata da Enzo Fernandez ba, wanda take ta nacin sai ta dauka a Janairun nan.

    Dan wasan tawagar Argentina yana da kunshin kwantiragin sama da fam miliyan 105, idan har kungiyar Stamford Bridge ta biya kudin zai zama mafi tsada a Premier League kenan.

    Enzo Fernandez

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Arsenal ta kara taya Caicedo na Brighton

    Brighton ta ki sallama tayi na biyu da Arsenal ta yi wa dan kwallon tawagar Ecuador, Moises Caicedo ta kuma ce bana sayarwa ba ne.

    An ce tayin ya kai fam miliyan 70.

    The latest bid is thought to be in the region of £70m.

    Arsenal da Chelsea na rububin daukar dan wasan mai shekara 21 kafin ranar talata a rufe kasuwar cinikayyar 'yan wasa ta Turai.

    Sai dai bai buga wa Brighton FA Cup da ta doke Liverpool 2-1 ranar Litinin ba.

    Moises Caicedo

    Asalin hoton, Getty Images

  19. Nottingham Forest za ta dauki Shelvey na 25 a bana

    The Telegarph ta bayar da rahoton cewar Janjo Shelvey zai koma taka leda a Nottingham Forest, zai zama na 25 da za ta dauka tun bayan da ta koma buga Premier League a bana.

    Janjo Shelvey

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Jama'a barkanmu da kasancewa a cikin shirin labarin wasanni kai tsaye.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW zan gabatr muku da shirin.

    Za ku iya bayar da gudunmuwa a lokacin da muke gabatar da shirin a BBC Hausa Facebook da kuma a Twitter.