Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Everton ta kammala daukar Dwight McNeil
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.
Rahoto kai-tsaye
Mohammed Abdu
Ko De Jong ya zabi ci gaba da taka leda a Barca ne?
Har yanzu Manchester United ba ta hakura da zawarcin Frenkie de Jong ba daga Barcelona, wanda take fatan saya a kakar nan, in ji Give Me Sport.
Tawagar kwallon kafa ta Ghana za ta buga wasan sada zumunta da ta Switzerland a United Arab Emirates a shirin tunkarar gasar kofin duniya.
Za su fafata ranar 17 ga watan Nuwamba a filin wasa na Baniyas da ke Abu Dhabi, kuma karon farko da za su fara haduwa a tsakaninsu a fagen taka leda.
Batun da kuke tafka muhawara a BBC Hausa Facebook
Ana ta alakanta dan kwallon Brazil, Antony da cewar zai koma Manchester United a bana don ci gaba da taka leda da takwaransa Martinez domin ci gaba da taka leda karkashin Erik ten Hag a Old Trafford.
Sai dai kamar yadda the Mail, ta wallafa ta ce Ajax ta kara farashin dan wasan zuwa fam miliyan 84 karin fam miliyan 16 kudin farko da ta bukata.
Shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya, Amaju Pinnick ya ce suna kokarin karbar bakuncin gasar kofin nahiyar Afirka a 2025 - sai dai hukumar kwallon kafa ta Afirka Caf ta nanata cewar dama ce ta kasar Guinea.
Pinnicks ya sanar da cewar ya shaidawa babban kwamitin Caf a wani taro da suka yi ta Intanet cewar Najeria tana da sha'awar karbar bakuncin gasar da za a yi a 2025 tare da yin hadaka da Benin.
Sai dai kuma yanayin rashin kwanciyar hankali da 'yan siyasa suka jefar kasar, inda sojoji suka yi juyin mulki a bara ya sa fargabar tsaro ga masu gudanae da gasar tamaula ta Afirka.
Wasu rahotanni na bayar da sha'awar a dauke wasan daga kasar tun lokaci bai kure ba, amma Caf ta ce haka za a yi wasannin a kasar.
A Janairun 2019 hukumar kwallon kafar Afirka ta yi Guinea ta yi karbar bakuncin gasar kofin Afirka a 2025, wadda ta amince da hakan.
Shin kun san ranar da za a fara La Liga a bana kuwa?
Labarai da dumi-dumi, Dwight McNeil ya koma Everton daga Burnley
Everton ta kammala daukar dan wasan Burnley mai taka leda daga tsakiya Dwight McNeil.
Ta sayi dan wasan kan yarjejeniyar kaka biyar kan kudi fam miliyan 20.
McNeil ya buga wasa 140 a Burnley ppearances, kuma wasa biyu kacal ne da bai buga ba a Premier League tun daga Disambar 2018.
Dan kwallon tawagar Ingila 'yan kasa da shekara 21 ya zama na biyu da ya koma Goodison Park, bayan James Tarkowski da kuma Ruben Vinagre da zai buga mata wasannin aro daga Sporting.
Aston Villa ta nada McGinn sabon kyaftin dinta
Kociyan Aston Villa, Steven Gerrard ya nada John McGinn kyaftin din kungiyar, domin maye gurbin Tyrone Mings, wanda Gerrard ya bukaci ya mayar da hankalinsa wajen bunkasa wasa, bayan da ba nauyi a kansa a yanzu.
Mings mai shekara 29 ya ce ya amince da wannan sauyin abu ne aka yi don ci gaban Aston Villa ba wani haufi a tare da shi.
Dan kasar Scotland, Sabon kyaftin McGinn, mai shekara 27, ya koma Aston Villa a 2018.
Shin ko Firmino zai amince ya koma Juventus?
Kaamr yadda According toCorriere dello Sport, ta ce Juventus na daf da kulla yarjejeniyar daukar dan wasan Liverpool, Roberto Firmino, mai shekara 30.
Idan har dan wasan ya amince ya bar Anfield, zai zama saura Mohamed Salah kadai daga gurmin masu cin kwallo uku da suka taka rawar gani a kungiyar karkashin Jurgen Klopp.
Sadio Mane ya bar Liverpool zuwa Bayern Munich.
Ko Juventus za ta hakura da daukar masu cin kwallaye a Premier League?
Wasu labaran da jaridun Italiya suka wallafa ya ce kokarin da Juventus ta fara na son daukar Firmino zai kawo karshen zawarcin dan wasan Manchester United, Anthony Martial da na Chelsea, Timo Werner.
Tun farko an alakanta 'yan wasan biyu da cewar za su koma Newcastle a kakar nan.
PSG ta ci karo da cikas kan cinikin Skrinia na Inter
PSG hit Skriniar ‘roadblock’
Will get their man?
Ko Ronaldo zai matsa sai ya bar Man Utd exit?
Ana ta wallafa labarai kan cewa makomar Cristiano Ronaldo a Manchester United.
The Mailare ta sanar cewar dan kwallon ya bukaci a soke sauran yarjejeniyar da ta rage masa a Old Trafford, amma har yanzu kungiyar ba ta samu sakon nan.
De Jong na son ci gaba da zama a Barca?
Frenkie de Jong daya ne daga cikin 'yan wasan da Manchester United ke son dauka a kakar nan, kuma har yanzu ba ta fitar da tsammani ba, in ji Give Me Sport.
To sai dai kuma Cadena Ser ta ce dan wasan ya sanar da Barcelona cewar yafi son cin gaba da taka leda a Barcelona.
Tawagar mata ta Ingila za ta sa kaya farare a wasan karshe da Jamus
Tawagar kwallon kafa ta mata ta Jamus mai rike da kofin nahiyar Turai takwas za ta buga wasan karshe da Ingila ranar Lahadi a Wembley a gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2022, bayan da ta doke Faransa a daf da karshe a Milton Keynes ranar Laraba.
Ingila wadda ke fatan lashe kofin a karon farko ta casa Sweden 4-0 a filin wasa na Sheffield United a Bramall Lane ranar Talata.
Bordeaux za ta buga gasar Faransa mai daraja ta biyu maimakon ta uku a bana
An yanke hukuncin cewar Bordeaux ta buga babbar gasar kwallon kafa ta Faransa ta biyu daf da za a fara kakar bana a karshen makon nan.
Bordeaux, wadda ta lashe Ligue 1 shida, ta yi ta karshe a kakar da ta wuce, sannan ta fada matsin tattalin arziki, bayan da bashi ya yi mata katutu.
Wani bincike da hukumar kwallon kafar Faransa ta sa ayi mata ya gano kungiyar ba za ta iya kasuwanci ba a kakar da za a fara, saboda haka aka turata buga karamar gasa mai daraja ta uku a kasar.
To sai dai an amince kungiyar ta buga gasa mai daraja ta biyu ta Faransa a kakar nan, bayan da shugabanta, Gerard Lopez ya zuba yuro miliyan 10 da samun yuro miliyan 14, kudin da suka sayar da 'yan wasa da zai sa ta iya gudanar da kasuwanci.
Bayern Munich ta kagu a fara Bundesliga a bana
Dina Asher-Smith ta hakura da wakiltar Burtaniya a gasar Commonwealth games ta bana.
Ta ji rauni ne a gasar tsalle tsalle da guje guje ta duniya - ta kuma sanar a kafarta ta sada zumunta cewar ba za shiga wasannin da za a yi a Birmingham.
Asher-Smith ta ci tagulla a tseren mita 200 a Commenwealth shekara hudu baya.
Za a yi bikin bude wasannin a yau Alhamis da fara fafatawa gadan gadan a gobe Juma'a.