Ko cinikin Williams zuwa Forest zai yi wu kuwa?
Sky Sports ta wallafa cewar sabuwar kungiyar da za ta buga Premier League a bana, Nottingham Forest ta kusan daukar Neco Williams kan fam miliyan 16.
Dan wasan tawagar Wales, wanda ya yi wasa 33 a dukkan karawa a Liverpool tun bayan da ya fara yi mata tamaula a Oktoban 2019 ya buga rabin kakar da ta wuce a Fulham a wasannin aro.