Nan muka kawo karshen shirin --
Da fatan za ku kasance da shiye-shiryen BBC Hausa a koda yaushe a Intanet da radiyo.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw ke cewa sai anjimanku.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.
Mohammed Abdu
Da fatan za ku kasance da shiye-shiryen BBC Hausa a koda yaushe a Intanet da radiyo.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tw ke cewa sai anjimanku.
Romelu Lukaku ya sake komawa Inter Milan domin buga mata wasannin aro kaka daya, bayan shekara daya da komawa Chelsea da taka leda.
Shin ko Lukaku zai taka rawar gani a Inter a kakar da za a fara?
Shin me ya hana shi kwazo a Chelsea ne duk da daukarsa da tsada a bara.
Celtic ta kammala daukar mai tsaron baya Alexandro Bernabei daga Atletico Lanus kan yarjejeniyar kaka biyar.
Dan kwallon tawagar Argentina ta matasa 'yan kasa da shekara 23 ya ci kwallo biyar a wasa 88 da ya yi wwa Lanus.
Juventus na ban kwana da Paulo Dybala da Alvaro Morata.
Andy Murray ya yi ban kwana da gasar kwallon tennis ta Wimbledon ta bana.
Zakaran gasar karo biyu ya sha kashi a hannun Jon Isner da ci 6-4, 7-6 (7-4), 6-7 (7-3), 6-4.
Kamar yadda Graeme Bailey of 90min ya sanar ya ce Newcastle da Tottenham da kuma Leeds United na rige-rigin daukar dan kwallon PSV Eindhoven, Noni Madueke.
Dan wasan mai shekara 20 ya ci kwallo uku ya kuma bayar da uku aka zura a raga a babbar gasar tamaula ta Netherlands da aka kammala.
Sven Botman daya ne daga fitatun masu tsaron baya a nahiyar Turai in ji wani mai labarin wasanni Luke Edwards.
Newcastle ta amince da kwantiragi da Lille kan daukar dan wasan mai shekara 22, wanda AC Milan ke son sayen dan kwallon.
A gasar kwallon golf Bryson DeChambeau ya ce kowa yana da damar yanke hukuncin shiga gasar Liv Golf.
Mai shekara 28 ya shiga sabuwar gasar da Saudi Arabia ke marawa baya a farkon watan nan tare da Brooks Koepka. a makon nan.
Za a gudanar da Liv Golf Invitational a Amurka, sannan a fafata a Portland, Oregon.
DeChambeau ya ce yana martabar 'yan wasan da su ka zabi ci gaba da buga PGA tour:
Daga yanzu duk mutanen da kotu ta yanke wa laifin da ya shafi cin zarafi a Intanet za a iya dakatar da su daga shiga kallon wasanni.
An fadada dokar bayan da masu shigar da kara suka bukaci daukar tsauraran matakan ladabtarwa da suka shafi cin zarafi a Intanet da ya hada da wariyar jinsi ko ta addini da keta mutunci.
A baya dokar ta shafi laifin cin zarafi gaba da gaba - Wani bincike da aka yi a 2021 ya gano cewar kaso 44 cikin 100 na 'yan wasan da ke buga Premier League sun fuskanci cin zarafi a Intanet.
A bazarar da ta wuce, gwamnati ta dauki alkawarin dakatar da mutanen da suka ci zarafin 'yan kwallo a Intanet zuwa shekara 10.
Hakan ya biyo bayan cin zarafin 'yan wasan tawagar Ingila da suka hada da Jadon Sancho da Bukayo Saka da kuma Marcus Rashford, wadanda suka kasa cin fenariti a Euro 2020, wanda Italiya ta lashe a Wembley.
West Ham za ta biya kudin warware cinikin Arnaut Danjuma na Villarreal, da suka kai fam miliyan 34. (Todofichajes - in Spanish)
Borussia Dortmund ta ce ba za ta karbi kasa da fam miliyan 103 ba kan dan wasan gabanta Jude Bellingham, wanda Liverpool da Manchester United da Real Madrid ke nema. (Bild via Mail)
Everton kuwa na son tsawaita zaman mai tsaron ragarta Jordan Pickford.(Guardian)
Arsenal ta mika tayin Lisandro Martinez ga Ajax a karo na uku, na fam miliyan 43.(Sun)
Chelsea tabi sahun jerin kungiyoyin da ke son daukar Raphinha daga Leeds United. Arsenal da Barcelona suka daga cikin fitattun da ke son daukar dan kwallon tawagar Brazil kafin fara kakar nan.
Leeds za ta bukaci fam miliyan 50, daidai da sama da naira biliyan 25 ga dan kwalon da ta dauka daga Rennes kan fam miliyan 17, kwatankwacin sama da naira biliyan takwas shekara biyu da ta wuce.
Sabon dan kwallon Bayern Munich, Sadio Made ya ce kungiyar Jamus tana kan turbar taka rawar gani a Champions League a bana, bayan da Villareal ta fitar da ita a quarter-final a bara.
Ya kara da cewar Bayern ta yi duk abinda ya kamata, amma hakanta bai kai ga cimma ruwa ba, ya ce ya san radadin da ya ji a lokacin da Atletico Madrid ta fitar da Liverpool - sai dai yana sa ran sabuwar kungiyarsa za ta lashe kofin kakar da za a fara.
Karo biyu a jere ana fitar da Bayern a daf da na kusa da na karshe, bayan da Paris Saint-Germain ta yi waje da ita a 2021, shekara daya da ta doke kungiyar Faransa ta dauki Champions Leafgue.
Za a ci gaba da sayar da sauran tikitin kallon wasannin gasar cin kofin duniya ranar 5 ga watan Yuli in ji hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa.
Za a iya sayen tikitin a shafin Fifa a Intanet - Qatar za ta karbi bakunci wasannin tsakanin 21 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disamba.
Tuni hukumar Fifa ta sayar da tikiti miliyan daya da dubu 800.
Kazalika United na son taya dan wasan tsakiyar Leicester City Youri Tielmans. (Times - subscription required)
Shi kuwa golan Man United din Dean Henderson zai tafi aro Nottingham Forest a matsayin aro.(Mail)
Arsenal kuwa ta tattauna da tsohon dan wasan tsakiyarta, yayin da take neman wanda zai horar da 'yan wasanta 'yan kasa da shekara 23 da 18.(Standard)
Lokacin da Shugaban riko na kungiyar kwallon kafa ta kano Pillars Alhaji Ibrahim Galadima yake jawabi ga Yan wasan kungiyar kwallon kafan ta kano Pillars a safiyar Alhamis a filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata Kano.