Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ajax ta tsuga farashin Anthony, yaya batun zuwan Jong United?

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan cefanen 'yan kwallo da labarin wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Labaran da jaridu ke wallafawa da suka shafi cinikin 'yan kwallo, Daga Jaridu

    Jaridar(Mirror)ta ce babu tabbas ko United na iya daukar Antony a yanzu, bayan da Ajax ta nemi fam miliyan 70 kansa.

    Ita kuwa Newcastle na dab da kammala cinikin mai tsaron bayan Lille Sven Botman kan fam miliyan 32, don mayar da hankali kan buda cinikin dan wasan gaban Reims Hugo Ekitike duk dai a Faransa.(Mail)

    Ana hasashen PSG za ta nada Christophe Galtier a matsayin sabon koci don maye gurbin Mauricio Pochettino, wanda ake sa ran ya bar kungiyar duk da lashe kofin gasar League 1.(ESPN)

    Barcelona ta shirya kyale Ousmane Dembele ya bar kungiyar, idan kwantiraginsa ta kare a ranar 30 ga watan Yuni. Tuni Bayern Munich da Chelsea da kuma PSG suka nuna sha'awar kulla yarjejeniya da shi.(Marca)

  2. Djokovic ya fara kare kofinsa na Wimbledon Open

    Mai rike da kofin Wimledon Open, Novak Djokovic ya fara kare kambinsa da kafar dama, bayan da ya casa Kwon Soon-woo a wasan zagayen farko da suka kece raini.

    Djokovic mai fatan lashe kofi na bakwai jumulla a gasar da ake yi a kan ciyawa, zai zama saura daya ya tarar da Roger Federer a tarihin yawan lashe wasannin.

    Dan kasar Serbia ya yi nasara a kan dan kasar Koria ta Kudu da ci 6-3 3-6 6-3 6-4, kuma wasa na 22 da ya ci a jere a gasar ta Wimbledon mai dan karen farin jini.

  3. Real Madrid ta samu karin magoya baya miliyan 1.7 a kafar sada zumunta

    Real Madrid ta samu karin magoya baya a kafar sada zumunta da suka kai miliyan 1.7 a Twitter da Facebook da Instagram da kuma YouTube a makon da ta lashe Champions League na 14 in ji wani bincike daga Blinkfire Analytics.

    Wannan kididdigar ta haura zakarun da suka lashe Champions League da suka hada da Chelsea da Bayern da kuma Liverpool.

    Tun daga 2018 da Real Madrid ta lashe Champions League na 13 a birnin Kiev, ba wata kungiyar da ta samu tarin magoya baya a kafar sada zumunta fiye da kungiyar Santiago Bernabeu.

  4. Kevin de Bruyne ya cika shekara 31 da haihuwa

    An haifi Kevin De Bruyne ranar 28 ga watan Yunin 1991, yana da shekara 31 kenan.

    Ga jerin kungiyoyin da ya buga wa tamaula

    Matashin dan wasa

    1997–1999 KVV Drongen

    1999–2005 Gent

    2005–2008 Genk

    Kwararren dan kwallo

    2008–2012 Genk

    2012–2014 Chelsea

    2012–2013 Wasannin aro a Werder Bremen

    2014–2015 VfL Wolfsburg

    2015–Manchester City

    Tawagar Belgium

    2008–2009 Belgium U18

    2009–2010 Belgium U19

    2010–2011 Belgium U21

    2010–Belgium

  5. Tottenham na neman 'yan wasan Everton biyu, Tottenham

    Sky Sports ta wallafa cewar Tottenham na fatan sayen dan kwallon Everton, Richarlison - ta kuma kara da cewar kungiyar da Antonio Conte ke jan ragama tana kuma da burin daukar Anthony Gordon.

  6. Fernandinho da Sterling da Gabriel Jesus

    Bayan da Fernandinho ya bar Manchester City, Raheem Sterling da Gabriel Jesus na shirin barin Etihad - ko yaya Pep Guardiola zai sauya wasanninsa a kungiyar.

  7. Barkanmu da kasancewa

    Jama'a barkanmu da kasancewa a shirin labaran wasanni da yadda kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ke gudana a rana irin ta yau.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper zan gabatar da shirin da fatan za ku kasance da BBC Hausa a koda yaushe.

    Za ku iya bayar da gudunmuwa ko tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko a Twitter.