Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Real Madrid ta bai wa Barcelona tazarar maki biyu

Wannan shafi ne kai tsaye da ke dauke da labarin wasanni da ake fafatawa a karshen mako musamman wasan Espanyol da Real Madrid.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan na kawo karshen shirin

    Da fatan za ku tara a wani shirin na gaba.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper ke muku fatan alheri.

  2. An tashi wasa - Espanyol 0-1 Real Madrid

    Real Madrid ta hada maki uku ta kuma koma ta daya a teburin La Liga.

    Idan har za ta cinye dukkan wasanninta shida da suka rage to za ta lashe kofin La Liga na bana.

    Barcelona ce ke rike da kofin bara na La Liga.

  3. Espanyol 0-1 Real Madrid

    Real Madrid ta samu bugun tazara amma sai ba ta lokaci take yi.

    Marcelo ya buga ta kusan ta bugi dan wasa ta fada raga.

  4. Espanyol 0-1 Real Madrid

    Espanyol ta kusan farke kwallo Marc Roca ne ya yi bugun tazara mai kyau

    Sai Bernardo Espinosa ya sa aki ta je wajen Leandro Cabrera shi kuma bai yi caca ba ya buga kwallon ta bugi raga ta wajen fili.

  5. Katin gargadi - Espanyol 0-1 Real Madrid

    An wa dan kwallon Real, Vinicius Jr katin gargadi bayan da ya tare Oscar Melendo.

  6. Espanyol 0-1 Real Madrid

    Bayan Real Madrid a dinke yake a wasan nan ko za ta rike maki ukun nan? Ya kamata ta kara na biyu ko hankali ya kwanta.

  7. Canji na karshe da Espanyol ta yi

  8. Espanyol 0-1 Real Madrid

    An ci gaba da wasa kusan minti uku amma babu wani abu mashahuri da ya faru.

  9. Espanyol 0-1 Real Madrid

    Lokaci da za a sha ruwa sannan a koma wasa.

  10. Man Utd za ta kara da Chelsea a wasan daf da karshe a FA Cup

    Manchester United za ta fafata da Chelsea, inda Arsenal za ta fuskanci mai rike da kofi Manchester City a wasan daf da karshe a FA Cup.

    An raba jadawalin ne mai dauke da kungiyoyi uku da ke kan gaba a yawan lashe FA Cup har da Arsenal mai 13 jumulla.

    • Ceballos ya kai Arsenal wasan daf da karshe a FA Cup
    • Chelsea ta kai daf da karshe a FA Cup, bayan da ta ci Leicester City

    United, wacce ta doke Norwich City ta kai wannan matakin tana da shi 12 jumulla, ita kuwa Chelsea da ta ci Leicester City tana da shi guda takwas.

    Za a buga dukkan wasan daf da karshe a Wembley a karshen makon 18 da kuma 19 ga watan Yuli.

    An tsayar da ranar 1 ga watan Agusta domin buga wasan karshe a Wembley.

    An raba jadawalin ne a lokacin da aka yi hutu a wasan da Newcastle United ke karbar bakuncin mai rike da kofin Manchester City, kuma City ce ta yi nasara da ci 2-0.

    Arsenal wacce take kan gaba a lashe FA Cup ta kai fafatawar daf da karshe a bana, bayan da ta ci Sheffield United 2-1, kuma Dani Ceballos ne ya ci mata na biyun a minti na 91.

    Wasan daf da karshe tsakanin United da kuma Chelsea maimaicin karawar karshe kenan da suka yi a 2018, inda kungiyar Stamford Bridge ta lashe kofin.

  11. Espanyol 0-1 Real Madrid

    Wani motsi da Espanyol ta yi mai kyau inda David Lopez daga yadi na 25 ya buga kwallo zuwa ragar Real Madrid, amma Thibaut Courtois ya tare da wata matsala..

  12. Katin gargadi - Espanyol 0-1 Real Madrid

    Daf da za a yi canji aka bai wa Adria Pedrosa kati mai ruwan dorawa bayan da ya yi wa dan kwallon Real Madrid, Dani Carvajal keta.

  13. Espanyol ta kara yin canji

  14. Espanyol 0-1 Real Madrid

    Real Madrid ta yi wasa 15 La Liga kwallo bai shiga ragarta ba a kakar bana inda 14 Thibaut Courtois ne ya tsare raga da daya da Alphonse Areola ya yi,.

    Wannan lokacin wanda ya yi wasa 16 kwallo bai shiga ragarsa ba shi ne Diego Lopez duk ya yi a Espanyol..

  15. Canjin Real Madrid

  16. Espanyol 0-1 Real Madrid

    Dan wasan Espanyol, Adrian Embarba ya bugo kwallo - ta dan kusan jawo rashin natsuwa a masu tsaron bayan Real Madrid nan da nan Raphael Varane ya buga kwallo ta yi tsiri sama shi kuwa mai tsaron ragar Madrid Thibaut Courtois ya kama cikin sauki.

  17. Chelsea ta kai daf da karshe a FA Cup, bayan da ta ci Leicester City

    Chelsea ta kai fafatawar daf da karshe a gasar FA Cup, bayan da ta ci Leicester City 1-0 a King Power a wasan da suka yi ranar Lahadi.

    Sai da suka yi mnti 45 ba ci aka je hutu, bayan da aka koma zagaye na biyu Frank Lampard ya sa Ross Barkley wanda ya ci mata kwallon.

    • Chelsea ta rama abin da Manchester City ta yi
    • Dalilin da Mertens bai koma Chelsea da taka leda ba

    Lampard da Chelsea na taka rawar gani tun lokacin da aka ci gaba da buga gasar Premier, inda kungiyar Stamford Bridge ta doke Aston Villa da Manchester City.

  18. Wani canjin na Espanyol

  19. Espanyol 0-1 Real Madrid

    Toni Kroos dauke da tamaula ya kuma buga da wuri kar a kwace sai dai ta yi saman raga.

  20. Espanyol 0-1 Real Madrid

    Real ta samu bugun tazara kuma Casemiro ne ya buga da karfi daga yadi na 35 sai dai ta bugi katangar da 'yan kwallo suka yi.