Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaushe ne Messi zai ci kwallo na 700?

Wannan shafi ne da ke dauke da labarin wasanni kai tsaye da ke zuwa muku musammam don sanar da ku abubuwan da ke faruwa a karshen mako a fagen wasanni

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Yaushe ne Messi zai ci kwallo na 700?

    Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga, bayan da ta doke Leganes da ci 2-0 a wasan mako na 29 da suka kara ranar Talata a Camp Nou.

    Matashin dan wasa dan kasar Guinea-Bissau Ansu Fati shi ne ya fara cin kwallo daga baya Messi ya kara na biyu a bugun fenariri.

    Kyaftin din Barcelona ya ci kwallo na 699 a Barca da tawagar Argentina a bugun fenariti, bayan da Ruben Perez ya yi masa keta a cikin da'irar Leganes.

    Barcelona ta je gidan Sevilla ta kuma tashi ba ci.

    Shin yaushe ne Messi zai ci kwallo na 700 kuma a wane wasan ne?

  2. Barcelona ta yi wasa hudu kwallo bai shiga ragarta ba

    Barcelona ta yi wasa hudu a gasar La Liga ta bana ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba.

    Na farko 1-0 da ta doke Real Sociedad tun kan a dakatar da wasanni saboda bullar cutar korona.

    Bayan da aka ci gaba da wasannin ban ne ta doke Mallorca 4-0 da kuma cin Leganes 2-0 da yin canjaras da Sevilla ranar Juma'a.

    Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga ta kuma yi karawa 14 kwallo bai shiga ragarta ba a hana, inda wasa 11 a La Liga ne da biyu a Champions League da daya a Copa del Rey.

    Haka kuma kwallo 34 ne ya sgiga ragar golan Barcelona, Marc-André ter Stegen a wasa 37 da ya yi.

  3. Saura wasa daya a kammala karawar Asabar a Premier

  4. West Ham 0-2 Wolves

    Wolverhampton ta yi wasa 10 a Landan ba a doke ta ba, inda ta ci biyar da canjaras biyar.

    Wacce ta haura ta ita ce Manchester United har karo biyu wasa 13 a Disambar 2013 da karawa 11 a Satumbar 2003.

  5. West Ham 0-2 Wolves, Pedro Neto

  6. Bale zai buga wa Real wasa da Sociedad

  7. An bukaci Neymar ya biya Barcelona fam miliyan 6.1

    An bukaci dan kwallon Paris St-Germain, Neymar da ya biya Barcelona fam miliyan 6.1 in ji wani hukunci da wata kotu a Spaniya ta yanke.

    Dan kwallon Brazil ne tun a baya ya ce yana bin kudi ladan wasa da ya kai Yuro miliyan 43.6 tun kan ya bar Barca a Agustan 2017.

    Neymar wanda ya shigar da karar bayan da zai koma PSG zai iya daukaka kara kan hukuncin da aka yanke.

  8. Lewandowski da Haaland kowa ya ci kwallo bibiyu a wasan Asabar

    Robert Lewandowski ya ci wa Bayern Munich kwallo biyu haka Erling Braut Haaland ya ci wa Borussia Dortmund biyu a wasannin karshe a gasar Bundesliga da aka kammala ranar Asabar.

    Bayern wadda tuni ta lashe Bundesliga na bana kuma takwas a jere na 30 jumulla ta yi nasara a kan Freiburg da ci 3-1 a anar Asabar.

    Dortmund ta kammala kakar bana a mataki na biyu, yayin da ta doke RB Leipzig 2-0 a wasan karshe.

  9. Ra'ayinku ta BBC Hausa Twitter

  10. Ra'ayinku ta BBC Hausa Twitter

  11. Sakamakon wasannin Championship

  12. West Brom ta koma ta daya a teburin Championship

    West Bromwich Albion ta koma buga gasar Championship, bayan kwana 105 da aka dakatar da wasanni saboda bullar cutar korona.

    Sai dai kungiyar ta tashi wasan hamayya da Birmingham City, kuma hakan ne ya sa ta koma ta daya a kan teburin Championship.

    Albion ta kai hare-hare 18 amma daya ne kacal ya nufi raga.

  13. Rostov ta je ta ci Sochi 10-1 a Premier Rasha

    Ranar Juma'a n a gasar Premier ta Rasha Rostov ta je ta zura wa Sochi kwallo 10-1.

    Tun kafin a ci gaba da gasar kwallon kafar kasar sai a Rotov ta killace 'yan wasa shida bayan da aka same su dauke da cutar korona.

    Wanan shi ne na wasa na biyu da aka buga a gasar kwallon kafar Rasha, tun bayan da aka dakatar da wasanni a cikin watan Maris saboda tsoron yada cutar korona.

  14. Brighton 2-1 Arsenal

    An ci Arsenal kwallo na biyu ne a minti 94 da dakika 26, kuma Neal Maupay ne ya ci wa Brighton kwallo mai mahimmaci da ya bai wa kungiyar maki ukun da take bukata.

  15. Yadda kungiyoyin suka muza leda

  16. Brighton 2-1 Arsenal

    Brighton na cin kwallo na biyu alkalin wasa ya hura tashi kuma Neal Maupay ne ya ci kwallon nan da nan 'yan wasan Gunners suka zagaye shi domin yana da hannu a raunin da golan Arsenal, Bernd Leono ya yi.

  17. GOAL - Brighton 2-1 Arsenal, Neal Maupay

  18. West Ham v Wolves

  19. Brighton 1-1 Arsenal

    Rabon da Alexandre Lacazette ya ci kwallo a wasan waje a gasar Premier League tun ranar 9 ga watan Fabrairun 2019.

  20. Brighton 1-1 Arsenal, Lewis Dunk

    An karbi kwallon wasa ya koma 1-1