A nan na kawo karshen shirin da fatan za ku tara nan gaba.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW ke cewa sai da safe.
Wannan shafi ne da ke dauke da labarin wasanni kai tsaye a karawar La Liga tsakanin Real Madrid da Valencia da wainar da ake toyawa a fannin wasanni a duniya
Mohammed Abdu
A nan na kawo karshen shirin da fatan za ku tara nan gaba.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW ke cewa sai da safe.

Asalin hoton, BBC Sport
Da aka koma zagaye na biyu ne Real ta bude wuta ta kara sa kwazo da hakan ya sa ta ci kwallo uku ta kuma hada maki uku.
Za a dauki shekaru da dama an tuna kwallon da Karim Benzema ya ci domin ta kayatar matuka.
Kai tsaye aka bai wa dan wasan Valencia, Lee Kang jan kati.
Kuma mintinsa 12 da ya canji dan wasa yanzu kuma ya fita daga karawar, koda yake ana daf da tashi da ya zawo musu wata barakar.
Kai tsaye ya nufi Sergio Ramos ya doka bayan da ko kusa ba kwallo a kusa, ya kamata kam ya fita daga karawar.
Karim Benzema ne ya maki kwallo da kafarsa ta shi ragar Valncia ta wajen makogwaro daga bangaren hadu, kuma Marco Asensio ne ya ba shi fasin.
Goaln Valencia, Jasper Cillessen ya kara hana kwallo ya shiga raga.
Wannan karon Toni Kroos n ya so ya ci shi daga bugun tazara amma golan ya kula saboda haka sai ya yi wa kwallon gada ya yi waje.
Yanzu na gama maganar Hazard.
Dan kwallon Belgium ya fita kuma Vinicius Jnr on ya maye gurbinsa..
Eden Hazard na dan yi dari dari tun bayan da ya warke daga jinya sai dai kocin Real, Zinedine Zidane yana ta bai wa dan kwallon lokaci kan ya koma ganiya.

Asalin hoton, Getty Images
Dn wasan Valencia. Lee Kang ya canji Rodrigo Moreno.
Kwallon farko da ya zura a raga a kakar bana.
Marco Asensio ya buga kwallo da kafarsa da kafarsa ta hagu ta bi ta tsakiyar ragar Valencia, kuma ya samu kwallon daga Ferland Mendy .
Real Madrid ce ke kai kora ko za ta ci kwallo na biyu.
Luka Modric ne ya samu kwallo ya buga da kafar hagu ta je wajen gola Jasper Cillessen ya yi kokarinsa..
Sa 10 kenan dan wasan tawagar Netherlands na tare kwallo.
Kwallon nan ta kassara Valencia.
Real Madrid ta i wasa 13 ba a zura mata kwallo a raga ba a kakar bana.
Hakan na nufin fiye da 12 da ta yi a gaba dayan kakar bara.
Luka Modric ne ya bai wa Eden Hazard, wanda ya rike ya yanke dan kwalon Valencia daga nan ya bai wa Benzema kwallo wanda babu kowa a wajensa shi kuwa ya zura a raga.
Tun da aka koma zagaye na biyu Real ce ta ke ta sa kwazo.
Federico Valverde ne daga yadi na 25 ya buga kallo amma golan Valencia, Jasper Cillessen ya kama ta gam.
Dan wasan Real, Daniel Carvajal ya buga kwallo daga waje da kafarsa ta hagu amma an tare kuma Luka Modric ya ba shi kwallon.
Daniel Wass na Valencia ya samu bugun tazara daga bayan Real Madrid gaba-gaba kadan.
Sergio Ramos kyaftin din Real Madrid ya yi keta.
Cikin natsuwa Real Madrid tana higa bayan Valencia amma ba sa yin abin da zai ba su naki uku a yanzu dai.
Shi kansa Toni Kross bai samu wani sarari da zai tura kwallo tsakanin 'yan bayan Valencia ba.
Hakika Valencia ta shirya wa wannan karawar.
An koma zagaye na biyu.
Real Madrid na bukatar maki uku a wannan wasan kuma nan da minti 45 za a tantace.