Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Bayern Munich ta ragargaji Leverkusen da ci 4-2

Wannan shafi ne da ke dauke da labarin wasanni da ke gudanar a karshen mako don sanar da ku irin wainar da ake toyawa kai tsaye.

Rahoto kai-tsaye

  1. kwallo a raga Dusseldorf 1-1 Hoffenheim, Munas Dabbur

  2. Jan kati Dusseldorf 1-0 Hoffenheim

    Dusseldorf ta samu kwarin gwiwa bayan da aka bai wa mai tsaron bayan Hoffenheim, Benjamin Hubner jan kati saboda gula da ya yi.

  3. Leverkusen 1-0 Bayern, Lucas Alario

  4. Dusseldorf 1-0 Hoffenheim, Rouwen Hennings

    Lucas Alario ne ya fece a guje ya kuma wuce Jerome Boateng sannan cikin ruwan sanyi ya saka kwallo a ragar Bayern Munich. Kuma na'urar da take taimakawa alkalin wasa yanke hukunci ta amince da kwallon.

  5. Leverkusen 0-0 Bayern

    Dan wasan Leverkusen wanda ya ji rauni Kai Havertz yana zaune a gefe yana kallon wasan da takunkumi rufe fuska.

    A kaka uku baya wasa hudu ne bai buga ba daga 96 a Bundesliga saboda jinya har da karawar yau.

  6. Leverkusen 0-0 Bayern

    Alphonso Davies ya kai wata karamar kora, amma Leverkusen na kara matsawa Bayern dalilin da ya sa suka koma baya kenan don hana kai wa wajen mai tsaron raga Manuel Neuer.

  7. An take wasa Leverkusen v Bayern

  8. Frankfurt v Mainz

    Dan wasan Liverpool, Taiwo Awoniyi, wanda ya je Jamus buga wasannin aro zai buga fafatawar yau..

  9. Frankfurt da Mainz

    Wadanda za su buga wa Mainz karawar.

  10. Ko Lewandowski zai haura Muller a cin kwallaye a Bundesliga?

    An ci gaba da buga gasar Bundesliga tun cikin watan Mayu don karkare wasannin 2019-20 da cutar korona ta kawo tsaiko.

    Kawo yanzu an buga wasa uku kuma 29 jumulla, saura karawa biyar a kammala gasar kasar Jamus ta bana.

    • Coronavirus: Lewandowski ya bada gudunmuwar Euro miliyan daya
    • Lewandowski ya ci gaba da jan ragama a cin kwallo a Bundesliga

    Kawo yanzu dan wasan Bayern Munich, Robert Lewandowski ne ke kan gaba da kwallo 29, bayan wasannin mako na 29, shin ko Lewandowski zai haura Gerd Muller a cin kwallaye a wasannin?

  11. Leroy Sane zai koma Bayern Munich

    Dan wasan Manchester City, Leroy Sane zai saka hannu kan yaejejeniyar shekara biyar da kungiyar Bayern Municha in ji jaridar Jamus wato Bild.

  12. Bayern Leverkusen da Bayern Munich, Wadanda za su buga karawar

    Leverkusen: Hradecky - Tapsoba, S. Bender, Dragovic - Amiri, Aranguiz, Baumgartlinger, Bailey - Bellarabi, Alario, Diaby

    Masu jiran ko ta kwana: Özcan, Tah, Paulinho, Demirbay, Wendell, Weiser, Palacios, Wirtz, VollandKoci: Peter Bosz

    Bayern: Neuer (c) - Pavard, Boateng, Alaba, Davies - Kimmich, Goretzka - Gnabry, Müller, Coman - Lewandowski

    Masu jiran ko a kwana: Ulreich, Odriozola, Thiago, Martinez, Perisic, Hernandez, Singh, ZirkzeeKoci: Hansi Flick

  13. 'Yan kasan teburi bayan wasannin mako na 29

  14. 'Yan saman teburi bayan wasannin mako 29

  15. Lewandowski ne kan gaba a cin kwallaye a Bundesliga

    • Robert Lewandowski Bayern Munich 29
    • Timo Werner RB Leipzig 25
    • Jadon Sancho Borussia Dortmund 17
    • Robin Quaison Mainz 12
    • Sebastian Andersson FC Union Berlin 12
    • Jhon Cordoba FC Koln 12
    • Rouwen Hennings Fortuna Dusseldorf 12
    • Marco Reus Borussia Dortmund 11
    • Serge Gnabry Bayern Munich 11
    • Wout Weghorst Wolfsburg11
    • Florian Niederlechner FC Augsburg 11
    • Kai Havertz Bayer 04 Leverkusen 11
  16. Sakamakon wasannin mako na 29 a Bundesliga

  17. Wasannin Bundesliga na ranar Asabar mako na 30

  18. Za a ci gaba da wasannin Bundesliga karawar mako na 30

    Idan anjima ne za a ci gaba da gasar Bundesliga karawar mako na 30, bayan da Bayern Munich ke jan ragamar teburin gadar.

    Haka kuma Bayern Leverkusen tana da damar taka rawar gani a wasannin makon nan har da Borussia Monchengladbach da Dortmund da kuma RB Leipzig.

  19. Jama'a barkanmu da saduwa cikin shirin labarin wasanni kai tsaye na karshen mako, inda zan dinga sanar da ku abubuwan da ke wakana a wannan lokacin.

    Yau za a ci gaba da wasannin mako na 30 a gasar Bundesliga ta Jamus.

    Cristiano Ronaldo ya zama biloniya

    Chelsea ta kulla yarjejeniyar sayen Timo Werner

    Ko yaushe ne za a ci gaba da gasar Firimiyar Nigeria.

    Wadannan da sauran batutuwa ne zan gabatar muku da fatan za ku kasance da shirin.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper zan gabatar muku da shirin.