Tottenham ta karbo bashin fam miliyan 175 daga bankin Ingila, don shawo kan matsalar tattalin arziki da ake fuskanta saboda cutar korona.
Tottenham ta yi kiyasin cewar za ta rasa fam miliyan 200 idan aka ci gaba da buga Premier ba 'yan kallo a filinta mai cin mutum 62,303, an kuma soke wasu wasannin na da ban.
Kungiyar ta cancanci karbar bashin a gwamnatance don shawo kan matsin tattalin arziki da ake fuskanta, kuma za ta biya kudin ruwa na kaso 0.5 cikin 100.
Tottenham wadda ke buga gasar Champions League a bana tana mataki na takwas a kan teburin Premier League.
Ranar 17 ga watan Yuni za a ci gaba da gasar Premier ta bana da kwantan wasa biyu tsakanin Aston Villa da Sheffield da na Manchester City da Arsenal.
Saura wasanni tara-tara suka rage wato jumulla 92 a karkare kakar 2019-20.