Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasan El Clasico a Camp Nou

Muna kawo maku wasan La Liga tsakanin Barcelona da Real Madrid kai-tsaye.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. , Barcelona 0-0 Real Madrid

    Wasan hamayyar El Clasico ya tashi babu ci a filin wasa na Camp Nou a wasan La Liga mako na 10.

    Wannan ne wasan Clasico na 90 da aka buga a Camp Nou kuma har yanzu kungiyoyin na kankankan a wurin nasara, inda kowaccensu ta ci wasa 72 a dukkanin wasannin Clasico na La Liga.

    Real Madrid ce ta kankane minti 45 na farko sakamakon kokarin da 'yan wasan tsakiyarta Tony Kroos da Valverde suka yi.

    Amma Barcelona ma ta kankane falle na biyu na wasan kafin Gareth Bale ya zira mata kwallo a raga, sai dai na'urar VAR ta ce Mendy ya yi satar gida, wanda shi ne ya bai wa Bale kwallon.

    An bai wa Barcelona katin gargadi sau uku a minti 45 na farko, abin da ke nuna cewa ba ta ji dadin zagayen ba.

    Ita kuwa Madrid an ba ta guda biyar kuma duka a minti 45 na biyu, abin da ke nuna ita ma ba ta ji dadin zagayen ba.

    Da ma dai tun kafin wannan wasan kungiyoyin ne a saman teburi da maki 35 kowaccensu, amma Barca tana saman Madrid da tazarar kwallo biyu.

    Haka abin zai ci gaba da kasancewa yayin da Barca za ta karbi bakuncin Deportivo Alaves ranar Asabar, Madrid kuma ta karbi bakuncin Athletic Club.

    Sevilla ce ke biye masu a mataki na uku da maki 31, yayin da babbar abokiyar hamayyarsu Atletico Madrid ke mataki na biyar da maki 29.

  2. Jadawalin La Liga, Barcelona 0-0 Real Madrid

  3. Wasa ya kare 90+5, Barcelona 0-0 Real Madrid

  4. Barcelona 0-0 Real Madrid, Barcelona 0-0 Real Madrid

    Da alamun wasa zai ci 'yan kallo.

  5. An kara minti, Barcelona 0-0 Real Madrid

    An kara minti biyar.

    Tuni minti 90 ya cika kuma har yanzu ba mu ga gwani ba a wannan wasa.

  6. Ansu Fati, Barcelona 0-0 Real Madrid

    Shekarar Ansu Fati 17 da kwana 48, ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya buga El Clasico a wannan karnin.

  7. Canji, Barcelona 0-0 Real Madrid

    Matashin dan wasa Ansu Fati ya karbi Griezmann.

  8. Madrid ta yi canji, Barcelona 0-0 Real Madrid

    An cire Valverde an sako Modric sai Isco da ya fita ya bai wa Rodrygo

  9. Katin gargadi, Barcelona 0-0 Real Madrid

    An bai wa Ramos katin gargadi. Da ma an saba ai.

  10. Katin gargadi, Barcelona 0-0 Real Madrid

    An bai wa Isco katin gargadi sakaamkon ketar da ya yi wa Griezmann.

  11. '74, Barcelona 0-0 Real Madrid

    Suarez ya tashi tsintsaye da kwallon da ya buga waje daga yadi na 10.

  12. '71, Barcelona 0-0 Real Madrid

    Courtois ya farga ya kama harin da De Jong ya buga masa ta-ci.

  13. Kwallo ta shiga amma an yi satar gida, Barcelona 0-0 Real Madrid

    Ana duba VAR domin tabbatar wa..... An yi satar gida kuma an kashe kwallon da Bale ya ci.

  14. Barcelona ta gaza katabus, Barcelona 0-0 Real Madrid

    Abin na neman zama abin kunya ga Barcelona an zo gidansu an fi su iya rawa.

  15. Haba Gareth Bale, Barcelona 0-0 Real Madrid

    Bale ya dada kwallo waje daga yadi na 8. Bale bai yi kokari ba gaskiya domin ya kamata a ce kwallon ta fi haka kyau.

  16. Katin gargadi, Barcelona 0-0 Real Madrid

    An bai wa Casemiro katin gargadi bisa ketar da ya yi wa Suarez, shi ne katin farko da aka bai wa Madrid.

  17. Messiiii, Barcelona 0-0 Real Madrid

    Saura kiris Messi ya saka kwallo a raga ba don matsi da Ramos ya saka masa ba, inda shi kuma ya harbi iska.

    Indai Messi na kai irin wannan korar to tabbas Madrid ba za ta sha ba.

  18. Marc Márquez, Barcelona 0-0 Real Madrid

    Abin girmamawa ne halartar Marc Márquez a filin wasa na Camp Nou. Shi ne zakaran tseren mota na duniya kuma sau 6 yana ziyartar filin wasa na Camp Nou din domin kallon wasan El Clasico.

  19. '58, Barcelona 0-0 Real Madrid

    Sargio Roberto ya dado kwallo daga bangaren dama amma Courtois ya kame ta babu wani hadari.

  20. Barcelona ta yi canji, Barcelona 0-0 Real Madrid

    An cire Nélson Semedo an sako Aturo Vidal