Liverpool 3-0 Man City, Liverpool 3-0 Man City
Wasan ya bude kowa na kai kora babu jin tsoro.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muna kawo maku sharhi da rahotanni kai-tsaye game da wasannin kwallon kafar Ingila na Premier League.
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Wasan ya bude kowa na kai kora babu jin tsoro.
Har yanzu magaoya bayan Liverpool ba su daina yi wa Sterling ihu ba, kuma fa a hakan ma sun ci wasa kenan. Me zai faru kenan da su ake ci?
Rodri ya karbi katin gargadi.
Henderson ya fita Milner ya shigo tare da karbar kambun kaftin.
Ana ta yi wa Pep ihu amma bai damu ba. Yana ta karawa yan wasansa karfin gwiwa na ganin sun rama kwallon da aka ci.
Liverpool ta hana City ta rika samun dama har takai da ta rama ko da kwallo daya daga cikin kwallon da aka ci ta.
Aikin ya kara kwabewa City ina mafuta?
Wanene ya yi saura akwai Agüero akwai Sterling akwai De Bruyne...
Sterling ya fara motsi kamar yadda ya kamata.
Abin da ake gudu ya faru anya City za ta farfado daga baccin da take?
Mane ya kara ta uku...
Yau dai Mane ya buya a wasan ba kamar yadda yake motsi ba a wasannin baya.
Da alamun City ta dawo da karfinta. Amma abin gudun shi ne kar ayi irin na wasan Wolves da Aston Villa su fita neman ci a karshe a zo a kara musu wata kwallon.
Mo Salah da abokan aikinsa ba za su huta ba sai sun tabbatar sun tafi da maki ukun nan domin dai ko ba komai sun san cewa magoya baya Premier League ne kawai a gabansu.
Duka bangarorin sun dawo cikin karsashi da kwarin gwiwa.. Liverpool na son kare kwallon da ta ci yayin da City ke neman farke kwallon da aka zira mata.
Idan City ta sake aka tashi haka to babu mamaki Liverpool ta dauki kofin Premier. Wa ya sani ne!
Pep Guardiola ya zaku a dawo ga shi nan a tsaye na jiran yan wasa su fito a ci gaba da wasa.
Leicester ce kawai za ta iya cinye Liverpool a yanzu.
Liverpool na kara tabbatr da matsayinta na babu wanda ya cinye ta a Premier bana, City na tsaka mai wuya ko don wajenta da za ta rasa a teburin gasar ta koma matsayi na 4.
Menene zai faru a rabin lokaci na biyu? sai mun gani ku kasance tare da mu har karshen wasan.
Filin wasa na Anfield ya harke da sowa yayin da kungiyoyin ke saka wa juna matsi.
Ana iya cewa ba a san maci tuwo ba gaskiya duk da cewa Man City ta fi taka rawa.
Fernandinho ya kwace kwallo mai kyau a hannun Salah.. da alama kuma Salah ya bugu a kafarsa ga shi nan dai a kwance.