Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda kasuwar sayen 'yan wasan Turai ta tashi

Muna kawo maku rahotonni kai-tsaye game da kasuwar saye da musayar 'yan wasa a nahiyar Turai, wadda ake rufewa a yau Litinin.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Kambun The Best Awards 2019 na kociyoyi, Sunaye ukun da ke kan gaba

    • ·Jurgen Klopp
    • ·Pep Guardiola
    • ·Mauricio Pochettino
  2. Kambun The Best Awards 2019 na maza, Sunaye ukun da ke kan gaba

    • Lionel Messi - Barcelona/Argentina
    • Cristiano Ronaldo Juventus/Portugal
    • Virgil Van Dijk - Liverpool/Netherlands
  3. Hernandez ya koma Sevilla, Kasuwar saye da musayar 'yan wasa

    Javier Hernandez ya zama dan wasa na 12 da Sevilla ta dauka a wannan kakar.

  4. Mkhitaryan ya koma Roma, Kasuwar saye da musayar 'yan wasa

    Dan wasan tsakiyar Armenia kuma dan wasan Arsenal Henrikh Mkhitaryan yana kan hanyarsa ta koma wa Roma a matsayin aro.

    Mkhitaryan ya shigo wasan Arsenal da Tottenham daga benci a wasan hamayyar da aka tashi 2-2 a Emirate jiya Asabar, kuma wannan ne wasansa na karshe a kulob din.

    Za a gwada lafiyar dan wasan mai shekara 30, inda zai hadu da tsohon abokin wasansa na Manchester United Chris Smalling.

    Roma ta tabbatar da isar dan wasan a babban birnin kasar Italiya.

    Wannan abu zai yi kyau sosai.

  5. Wasannin jiya, Lazio ta tsira da kyar a hannun Roma

    An raba maki a wasan hamayya tsakanin Lazio da Roma a wasan mako na biyu a gasar Serie A da suka kara ranar Lahadi.

    Roma ce ta fara cin kwallo ta hannun Aleksandar Kolarov a bugun fenariti, bayan da dan wasan Lazio, Sergej Milinkovic-Savic ya taba kwallo da hannu a da'ira ta 18.

    Tun farkon take kwallo Ciro Immobile da kuma Joaquin Correa sun buga tamaula ta bugi turke, haka kuma Nicolo Zaniola ya taka-ledar da ya gagari Roma.

    Lazio ta farke kwallo ne ta hannun Romero Alconchel, minti kadan bayan da aka koma hutu.

    Mai masaukin baki wato Lazio ta ci kwallo na biyu daf da za a tashi daga wasan, amma alkalin wasa ya ce an yi satar gida.

    Da wannan sakamakon Lazio ta koma ta biyu a kan teburin Serie A, ita kuwa Roma ta zama ta 11 a teburin gasar bana.

  6. Wasannin jiya, Arsenal vs Tottenham: Arsenal ta kauce wa abin kunya

    Arsenal ta kauce wa abin kunya a filin wasa na Emirate inda ta farke kwallo biyu da Tottenham ta zura mata a wasan mako na hudu na Premier ta bana, inda wasa ya tashi 2-2.

    Christian Eriksen ne ya fara jefa kwallo a ragar Arsenal din a minti na 10 bayan Bernd Leno ya dawo masa da kwallon da Lamela ya dada masa.

    A minti na 40 kuma Harry Kane ya kara ta biyu a bugun fanareti bayan Xhaka ya bige Son a cikin yadi na 18 din Arsenal.

    Ana daf da tafiya hutun rabin lokaci ne kuma Lacazette ya farke kwallon farko. Pepe ne ya ba shi kwallon shi kuwa ya take ta kuma ya shimfida ta raga.

    Pierre-Emerick Aubameyang ne ya farke ta biyun a minti na 71 bayan Guendouzi ya cilla masa kwallon ta saman 'yan bayan Tottenham, cikin sauki ya taba ta kuma ta zurare ta gefen Lloris zuwa raga.

    Ganin cewa kungiyoyin biyu 'yan arewacin birnin Landan ne, ana yi wa wasan lakabi da North London Derby wato wasan hamayyar arewacin Landan.

    Arsenal ta matsa zuwa mataki na 5 da maki bakwai yayin da Tottenham ta matso zuwa mataki na 9 da maki biyar.

    Game da wasan

    Sau biyu kacal Tottenham ta taba cin wasan Premier a gidan Arsenal a cikin wasa 27 da suka gwabza - 1993 da kuma 2010

    Tottenham din ce ta ci 2-0 a Emirate a Disambar da ya gabata a wasan League Cup.

    A dukkanin haduwa da suka yi sau daya Tottenham ta ci wasa a gidan Arsenal sau biyu a jere - a 1925 zuwa 1926

    An fi zura kwallaye ta hanyar fanareti a wasa tsakanin Arsenal da Tottenham da kuma wasa tsakanin Everton da Newcastle United.

    Wannan shi ne wasan hamayyar arewacin Landan na 186, inda Arsenal ta yi nasara sau 77 Tottenham kuma ta ci 58 kuma aka yi canjaras sau 51.

  7. Wasannin jiya, Gareth Bale ya tseratar da Real Madrid

    Real Madrid ta tashi 2-2 a gidan Villareal a wasan mako na uku a gasar cin kofin La Liga da suka fafata ranar Lahadi.

    Minti 12 da fara tamaula, Villareal ta ci kwallon farko ta hannun Gerard Moreno, sai dai Gareth Bale ya farke ta tun kan aje hutu.

    Bayan da aka dawo daga hutu ne Villareal ta kara na biyu ta hannun Moi Gomez, kuma Gareth Bale ne dai ya kara farke ta.

    Sai dai kuma Real ta karasa karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Gareth Bale jan kati daf da za a tashi daga fafatawar.

    Bale dan kwallon tawagar Wales ya zama na biyu a 'yan wasan Madrid, wanda ya ci kwallo biyu a wasa sannan aka bashi jan kati a karawar, bayan Cristiano Ronaldo.

    Wannan sakamakon ya kai Real mataki na biyar a teburin La Liga, ita kuwa Villareal tana ta 16 a wasannin shekarar nan.

    Ko a kakar bara kungiyoyin 2-2 suka taashi a gasar La Laliga, sai dai Real ta yi nasara da ci 3-2 a Santiago Bernabeu.

    Real za ta karbi bakuncin Levante a wasan mako na hudu ranar 14 ga watan Satumba, Villareal kuwa gidan Leganes za ta je a ranar.

    Yadda kungiyoyin suka murza-leda

  8. Kasuwar saye da musayar 'yan wasa

    Bisa tsari dai a ranar Asabar ne 31 ga watan Agusta ya kamata a rufe kasuwar a nahiyar Turai baki daya, amma saboda ta fado a cikin hutun karshen mako saboda haka sai yau a Litinin ne za a rufe ta.

    Lokutan rufewar ya bambanta daga kasa zuwa kasa kamar haka:

    Bundesliga 5:00

    Seria A 7:00

    La Liga da Ligue 11:00

    Scotland 12:00

  9. Barka da shigowa, Kasuwar saye da musayar 'yan wasa

    Masoya kwallon kafa barkanku da safiyar Litinin, da fatan kun shirya karbar sakamakon kasuwar saye da musayar 'yan wasan Turai da za a rufe a yau din nan.

    Umar Mikail ne ke maku barka da shigowa shafinmu na bayanai kai-tsaye game da 'yan wasan da za a saya da kuma wadanda za a bayar da aronsu.