Sai da safe
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Litinin idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Wannan shafi ne da zai rika kawo muku labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Litinin idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin agaji a Najeriya sun ce zuwa yanzu sun gano gawarwakin mutum goma sha biyar bayan da wani kwale-kwalen fasinja ya kife a ruwa a Lagos babban birnin kasuwancin kasar.
Sun ce a ranar Juma'a kwale-kwalen yake tafiya a kurarren lokaci sabanin doka, kuma igiyar ruwa ta gigita shi, lamarin da ya sa ya kife.
Wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su kananan yara ne wadanda ba sa sanye da rigunan kariya.
Ana yawan fuskantar haduran kwale-kwale a Najeriya saboda lodi fiye da kima, da kuma rashin lafiyar jiragen ruwa ko kuma kwale-kwale

Asalin hoton, Haramain Sharifain

Asalin hoton, Haramain Sharifain

Asalin hoton, Reuters
Rahotanni daga ƙasar Togo na cewa aƙalla yara bakwai ne bam ya kashe a ƙasar.
Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa wata irin ƙara ce ta tashe daga bacci a ranar Asabar a yankin Savanes da ke arewacin ƙasar.
Sojojin Togo na zaune cikin shiri tun bayan mummunan hari a karon farko da mayaƙa suka kai a watan Mayu, a lokacin da aka kashe sojoji takwas a kusa da iyakar ƙasar da Burkina Faso.
Mayaƙa masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da ƙungiyar IS da Al-Qaeda sun kai hari kan wurare da dama a ƙasashen Afrika.
Masu zabe a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo sun kammala kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokokin ƙasar.
Jam'iyyar Shugaba Denis Sassou Nguesso, wanda ya ke kan mulki kusan shekara arba'in, ita ake hasashen za ta samu mafi rinjayen kuri'un.
Wasu jam'iyyun adawa sun kaurace wa zaben sannan an kuma ruwaito cewa an samu karancin fitar jama'a a rumfunan zabe.

Asalin hoton, Getty Images
Jami'ai a Ukraine sun ce dakarun sojin kasar sun tarwatsa wani sansanin sojin Rasha a kudancin birnin Kherson da aka yi wa kawanya.
Wani mutmin mai suna Serhiy Bratchuk ya wallafa wani hoto da ya nuna hayaki na tashi daga yankin.
Gwamnatin da Rasha ta nada a birnin na Kherson ta amince da cewa an kai harin rokoki, sai dai sun ce asibiti da wani gida ne kawai harin ya shafa.
Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce dakarunta sun kai hari kan wata masana'anta a gabashin garin Slovyansk, inda suka kashe sojojin Ukraine da lalata harsasai.
Jami'an ceto a birnin Donetsk sun ci gaba da aikin duba wadanda suka tsira bayan da dakarun Rasha suka ruguza wani gida a Chasiv Yari ranar Asabar.
Akalla mutum 15 suka mutu sannan wasu 20 aka tabbatar da bacewarsu.

Asalin hoton, Reuters
Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken ya bukaci China da gabashin Asia da su matsa wa Myanmar wajen ganin ta mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da ta sanya wa hannu a shekarar da ta gabata.
Da yake magana a wata ziyara da ya kai Thailand, Mr Blinken ya ce bukatar China ce ta ganin Myanmar ta koma matsayin da take a baya kafin kifar da zababbiyar gwamnatin wajen a wani juyin mulki da sojoji suka yi a Fabrairun, 2021.
Mr Blinken ya kara da cewa kungiyar shiyyar da ke gabashin Asia, na bukatar ganin gwamnatin ta ɗabbaka yarjejeniyar da aka cimma da ita - wanda ya hada da kawo karshen tashin hankali a wajen da kuma tattaunawa da 'yan adawa.
Myanmar dai, ta kasance cikin rudani tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, inda ake gwabza yaƙi a cikin gida da kuma raba mutane da dama da muhallansu.

Asalin hoton, NDLEA
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta kama wani mutum bisa zargin safarar wata marainiya domin fitar da tabar wiwi zuwa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Jaridar Vanguard a Najeriya ta ruwaito cewa mutumin mai suna Matthew Bassey ya yi yunkurin fita da tabar ne ta hanyar saka ta cikin jakar marainiyar mai suna Peter Eno.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Mr Femi Babafemi ya fitar ranar Lahadi a Abuja, ya ce wanda suke zargin ya yaudari yarinyar ne da nufin sama mata aiki a kasar ta Dubai.
Hukumar ta ce ta kama kilo 2.80 na tabar wiwi a cikin jakar yarinyar wanda aka boye cikin kayan abinci.






Asalin hoton, bbc

Asalin hoton, PAVLO KYRYLENKO/REUTERS
Jami'ai a Ukraine sun ce akalla mutum 15 ne suka mutu bayan harin roka ta sama da Rasha ta kai kan wani gini a Chasiv Yar wani gari dake gabashin kasar.
Masu bayar da agajin gaggawa na kasar sun ce sun samu nasarar ceto muyum biyar da ransu.
Harin ya yi sanadiyyar rushewar bangare daya na ginin wanda ke kusa da birnin Kramatorsk da ke yankin Donetsk
gwamnan yankin Pavlo Kyrylenko ya tabbbatar da faruwar lamarin, inda ya ce Rasha ta yi amfani da manyan rokoki ne wajen kai harin.
Wani wanda ya tsallake rijiya da baya a harin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa sau uku abubuwan fashewa na fadawa kan ginin.

Asalin hoton, JAME JOEL
Gwamnatin jihar Lagas da ke kudu maso yammacin Najeira ta jajantawa mazauna unguwar Oko-Oba, a yankin Agege saboda ambaliya ruwan da suka fuskanta.
Abin da ya yi sanadiyyar bacewar mutum biyu tare da motocin da suke ciki a unguwar.
Ambaliyar ta faru ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tafka da safiyar jiya Asabar a yankin.
A wata sanarwa da kwamishinan kula da muhalli na jihar Tunji Bello ya sanya wa hannu , ya yi kira ga mazauna yankunan da su rika yin kaffa-kaffa tare da sanya idanu.
Jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar wato NEMA, sun ce sun samu nasarar kubutar da mutane hudu da ambaliyar ta yi awon gaba da motocinsu.

Asalin hoton, Buhari Sallau
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya sake jaddada kira ga hukumomin tsaro a kasar da su kara azama wajen kawo karshen matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.
A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai Malama Garba Shehu ya fitar, shugaban ya ce za a kawo karshen ayyukan ta'addanci da na 'yan bindiga ne kadai idan jam'an tsaron suka kara matsa kaifi.
Sanarwar ta kara da cewa duka 'yan bingidar da suka addabi kasar za su dandana kudarsu.
Daga karshe ya yi wa 'yan kasar addu'ar samun damina mai albarka.

Asalin hoton, AFP
Rahotanni daga Afirka ta Kudu na cewa akalla mutam14 ne suka mutu sakamon bude musu wutar da aka yi a wata mashaya da ke garin Soweto.
Wasu mutane 10 sun ji rauni, inda rahotanni suka rawaito uku daga cikinsu na cikin halin rai kwa-kwai mutu kwa-kwai a asibiti.
Kwamishinan 'yan sandan gundumar Gauteng, Elias Mawela, ya ce jami'an tsaro na wurin da lamarin ya faru a Nomzano Tavern da ke wajen birnin Johannesburg.
Ya kara da cewa, alamu sun nuna maharan sun afkawa mashayar ne tare da bude wa mashaya wuta.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Joe Biden, ya dauki matakin kare shirin balaguron da zai yi zuwa kasar Saudiyya a mako mai zuwa, wanda ya ce mutane da dama ba su amince da ita ba.
A wani bayani da aka wallafa a jaridar Washington Post, Mr Biden ya ce aniyarsa ita ce yaukaka dangantaka tsakanin kasashen biyu, ba tare da ya karya muradun Amirka ba.
Ya ce a bayyane ta ke karara baya goyon bayan cin zarafin dan adam, sannan batun 'yancin bildam na daga cikin muhimman batutuwan da za su tattauna da hukumomin Saudiyya.
Ya kafe kan tafiyar zuwa yankin gabas ta tsakiya na da muhimmanci, daidai lokacin da ake batun tsadar makamashi da kayan abinci da man fetur sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Masu bibiyarmu a wannan shafi na BBCHausa barkanmu da safiyar wannan rana ta Lahadi, ku kasance tare da mu a wannan shafi na domin sanin hakikanin abubuwan da ke faru a Najeriya da ma sauran sassan duniya.
Sunana Abdullahi Bello Diginza, ni ne kuma zan ja ragamar wannan shafi, za kuma ku iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta da muhawara domin bayyana ra'ayoyinku
