Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Yan Afirka ta Kudu sun fara jefa ƙuri'a a babban zaɓe

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 29 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Haruna Kakangi and A'isha Babangida

  1. Jonathan ya nuna damuwa kan sabon tsarin zaɓe a Afirka ta Kudu

    Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da ke jagorantar tawagar masu saka ido kan zaɓen Afrika ta Kudu ya bayyana damuwarsa kan sabon tsarin rajistar zaɓe na kasar.

    Ya shaida wa BBC cewa "abin da muke fargaba a kai shi ne mutanen da ba su koma yankunansu don kada kuri'unsu ba".

    "A da mutane na iya kaɗa ƙuri'unsu a manyan birane kamar Pretoria da Johannesburg da Cape Town ba tare da wata tangarda ba".

    "Amma a wannan karon, duk wanda yake son kaɗa ƙuri'a a inda ba mazabarsa ba na bukatar ya nemi hukumar zabe da ta sake masa mazaba zuwa inda yake son kada kuri'ar".

    Jonathan wanda ya jagoranci Najeriya daga 2010 zuwa 2015, ya ce da yawa daga cikin masu kada kuri'un ba su kammala wannan matakan ba, inda suke tunanin cewa za su iya yin zabe kamar yadda suka saba yi a baya.

    Jagoran mai shekara 66 ya kara da cewa: "Rudani kan kirkirar sabon tsarin zaɓe da aka yi don ba wa 'yan takara masu zaman kansu dama a karon farko a tarihin Afrika ta kudu na iya janyo matsaloli."

    Ya kuma ce ana bukatar wayar wa da mutane kai a mazaɓu wanda hakan zai kawo rashin sauri.

  2. Barcelona ta naɗa Flick a matakin sabon kociyanta

  3. Tinubu ya samu tarɓa da sabon taken Najeriya a majalisar dokoki

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa majalisar dokokin ƙasar domin ƙaddamar da ayyuka tare da yi wa majalisar jawabi a wani ɓangare na cikarsa shekara guda a kan mulki.

    Haɗakar majalisar dattawa da ta wakilan ƙasar ne suka tarbi shugaban a wani zaman haɗin gwiwa da suka gudanar.

    Majalisar ta tarbi shugaban ƙasar da tsohon taken ƙasar, wanda majalisar ta amince da sabon ƙudirin dokar da za ta sa a koma amfani da shi a faɗin ƙasar.

    Shugaban Majalisar Dattawan Godswill Akpabio ya ce da safiyar yau Laraba ne shugaban ƙasar ya saka hannu kan dokar komawa amfani da tsohon taken ƙasar.

  4. Ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya na son a binciki alƙalai a shari'ar masarautar Kano

    Shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya Nigerian Bar Association (NBA) ya ce za su binciki lauyoyin ɓangarorin da ke jayayya da juna a rikicin masarautar Kano da ke arewacin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa, Yakubu Chonoko Maikyau ya kuma nemi hukumar kula da harkokin shari'a ta ƙasa (NJC) ta binciki alƙalan da suka ba da umarni masu karo da juna kan rikicin masarautar.

    Tun da farko wata babbar kotun tarayya ta nemi a dakata da sauke Sarki Aminu Ado ko sauya dokar masarautun Kano har sai ta kammala sauraron ƙorafin da aka kai mata. Daga baya kuma wata babbar kotun Kano ta ba da umarnin kare Sarki Muhammadu Sanusi II kuma ta yi gargaɗin kada a fitar da shi daga gidan sarauta.

    Bugu da ƙari, babbar kotun ta Kano ta sake ba da umarnin bai wa Aminu Ado kariya da kuma gargaɗin kada a fitar da shi daga gidan sarauta. Sanusi na zaman fada a fadar Gidan Rumfa, yayin da Aminu ke nasa zaman a gidan sarki na Nassarawa.

    Ya ce abin da lauyoyin suka yi "ya jawo ƙasƙanci" ga ayyukansu kuma "za a ɗauki tsawon lokaci kafin a manta da irin abin kunyar da suka jawo".

    "Wannan abin takaici ne wanda kuma bai kamata ya faru ba tun farko," in ji shugaban NBA.

    "Saboda haka, NBA na kira ga shugabannin kotunan da abin ya shafa su ɗauki matakin gaggawa don gano ko lauyoyin ɓangarorin biyu sun aikata ba daidai ba kuma su aika wa hukumar kula da harkokin shari'a ta ƙasa rahoto don ɗaukar mataki."

  5. Kotu ta wanke shugaban Miyetti Allah daga zargin ta'addanci

    Babbar kotun tarayya a Abujan Najeriya ta wanke shugaban ƙugiyar Fulani ta Miyetti Allah, Bello Bodejo, daga zargin aikata ta'addanci da gwamnatin ƙasar ke yi masa.

    Cikin wani taƙaitaccen hukunci da Daily Trust ta ruwaito ta bakin kamfanin dillancin labarai na NAN, Mai Shari'a Inyang Ekwo ya wanke shi ne bayan lauyar ministan shari'a na Najeriya, Aderonke Imana, ta nemi janye tuhuma uku da suke yi masa.

    Lauyar ta faɗa wa alƙalin cewa Ministan Shari'a Lateef Fagbemi ne ya umarce ta ta janye ƙarar "bisa adalci".

    Ahmed Raji, wanda shi ne lauyan Badejo, bai ƙalubalanci ƙudirin janye tuhumar ba.

    Tun a watan Maris da ya gabata a gabatar da Bodejo a gaban kotun bisa zargin aikata ta'addanci bayan ya kafa wata ƙungiyar 'yan sa-kai a jihar Nasarawa.

  6. Ba mu kallon hare-haren Isra'ila a Rafah a matsayin cikakken farmaki - Amurka

    Mai magana da yawun fadar White House, John Kirby, ya ce Amurka ba ta kallon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa ta ƙasa a yankin Rafah a matsayin cikakken farmaki ba.

    Ya yi kalaman ne 'yan awanni bayan dakarun Isra'ila sun isa tsakiyar birnin har ma aka ce sun ƙwace iko da wani tsauni mai muhimmanci da ke kusa da iyakar Gaza da Masar.

    A farkon watan nan Shugaban Amurka Joe Biden ya ce zai dakatar da bai wa Isra'ilar makamai idan ta siga "yankunan gidajen mutane" a Rafah, inda dubban fararen hula ke samun mafaka.

    Isra'ila ta ce hare-haren sun kashe jagororin Hamas biyu, kuma suna da imanin cewa akwai yiwuwar wutar da ta tashi lokacin harin d aya kashe mutum 45 ranar Lahadi daga wani wurin ajiyar makamai ne na Hamas da ke kusa da wurin.

    Mista Kirby ya siffanta hotunan harin a matsayin "masu ban tausayi" da "tayar da hankali".

  7. Tinubu ya yi rawar gani a shekarar farko - Tijjani Gwarzo

    Ƙaramin minstan gidaje na Najeriya Abdullahi T Gwarzo ya bayyana cewa shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi ƙoƙari wajen daidata lamurran ƙasar duk da cewa babu wadatar kuɗi.

    Gwarzo na wannan bayani ne yayin da gwamnatin Tinubu ke cika shekara ɗaya a kan karagar mulki.

    A ranar 29 ga watan Mayu, 2023 ne aka rantsar da Tinubu bayan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa, sai dai ya karɓi mulkin ne a lokacin da ƙasar ke fuskantar ƙalubale masu yawa.

    Bayan karɓar mulkin nasa tattalin arziƙin al'umma ya ƙara taɓarɓarewa sanadiyyar tashin farashin kaya, wanda ya samo asali daga cire tallafin man fetur da kuma faɗuwar darajar naira.

    Sai dai Gwarzo ya ce "ai duk wanda ya san yadda aka zo aka samu ƙasar, ya ga kuma yadda ake ciki yanzu...an ci ƙarfin aiki, kullum ci gaba ake samu."

    Ya kuma ce gwamnatin ƙasar na gina gidajen masu ƙaramin ƙarfi a faɗin Najeriya waɗanda za a kammala a cikin wata uku.

    Kalli bidiyo domin ganin tattaunawar.

  8. Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara lalacewa a ƙarƙashin Tinubu - Atiku

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma jagoran adawa a Najeriya, Atiku Abubakar, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta APC, yana mai cewa sauye-sauyen tattalin arziki da ta ɗauka ba su sauƙaƙa wa 'yan ƙasa wahalhalu ba cikin shekara ɗaya.

    Jim kaɗan bayan rantsar da shi a kan mulki, Tinubu ya ƙaddamar da wasu jerin sauye-sauye da zimmar farfaɗo da tattalin arziki, waɗanda daga baya suka haddasa hauhawar farashi da kuma ƙunci a ƙasar baki ɗaya.

    Atiku ya ce tattalin arzikin ma baya ya koma a cikin shekara ɗaya ta mulkin Tinubu.

    "Kamar yadda muka yi tsammani, cikin wata 12, Tinubu bai cka alƙawarin farfaɗo da tattalin arziki da kawo ƙarshen wahalhalu ba," in ji shi cikin wata sanarwa da ya wallafa.

    "Matakan da ya ɗauka da waɗanda bai ɗauka ba sun ƙara ta'azzara tattalin arzikin Najeriya. Har yanzu ƙasar na fama kuma ta ma fi tangal-tangal a yanzu sama da shekara ɗaya da ta wuce.

    "Tabbas duka matsalolin - rashin aikin yi, da talauci, da wahalhalu - da suka mamaye gwamnatin Buhari sun ƙara ta'azzara."

    Idan ba a manta ba, daga cikin manyan matakan da Tinubu ya ɗauka har da sanar da cire tallafin man fetur a jawabinsa na rantsuwar kama aiki, kodayake rahotonni na cewa har yanzu gwamnati na biyan tallafin.

  9. Tarayyar Turai ta katse ƙawancen soji da Nijar

    Tarayyar Turai (EU) ta yanke shawarar kawo ƙarshen ƙawancen aikin soja da Jamhuriyar Nijar sakamakon juyin mulkin da sojoji suka tun a watan Afrilun 2023 da ya kifar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum.

    Shafin kafar yaɗa labarai ta Niger Focus ya ruwaito majalisar tarayyar na cewa ba za ta sabunta yarjejeniyar ba idan wa'adinta ya ƙare ranar 30 ga watan Yuni.

    An ƙaddamar da ƙawancen ne mai suna EUMPM a watan Disamban 2022 don ƙarfafa dakarun ƙasashen yankin Sahel saboda irin hare-haren da ƙungiyoyin IS da na al-Ƙa'ida ke kaiwa a yankin.

    A gefe guda kuma, Jamus ta ƙulla wata yarjejeniya da sojojin mulkin Nijar don cigaba da ayyuka a wani filin jirgin sama na birnin Yamai, kamar yadda shafin jaridar Der Spiegel ya ruwaito.

    Akwai sojojin Jamus kusan 90 a ƙasar.

    An tilasta wa dakarun ƙasashen Yamma ficewa daga Nijar ne yayin da mayaƙan ƙungiyar Wagner na Rasha ke shirin fara ayyuka, kamar yadda suka yi a Mali da Burkina Faso.

  10. Gwamnan Kano Abba ya haramta 'duk wani nau'i na zanga-zanga'

    Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya haramta gudanar “duk wani nau’in taro da zimmar zanga-zanga” a faɗin jihar yayin da ake ci gaba da tirka-tirka tsakanin sarakunan Kano biyu.

    Gwamnan ya yi iƙirarin cewa ‘yan jam’iyyar adawa na yunƙurin ɗaukar nauyin wasu ɗalibai daga wasu jihohi don tayar da hankali a jihar, kamar yadda mai magana da yawunsa Sanusi Bature ya bayyana cikin wata sanarwa a yau Laraba.

    “Gwamnan ya bai wa ‘yansanda, da ‘yansandan farin kaya, da jami’an tsaron Civil Defence umarnin kamawa da tsarewa da tuhumar duk wani mutum ko ƙungiya da suka shiga zanga-zanga a kan titunn Kano,” in ji sanarwar.

    Duk da cewa ana ci gaba da zama lafiya da kuma harkoki kamar yadda aka saba a birnin, kawunan Kanawan sun rarrabu game da sarkin da ke mulkin masarautar jihar tsakanin Muhammadu Sanusi II da kuma Aminu Ado Bayero.

    Yanzu haka kowannensu na da umarnin kotu biyu-biyu da ke hana jami’an tsaro fitar da shi daga fada ko kuma sauke shi a matsayin sarkin Kano. Sanusi na zaman fada a fadar Gidan Dabo, yayin da Aminu ke nasa zaman a gidan sarki na Nassarawa.

    A cewar Sanusi Bature, Gwamna Abba Kabir ya ce: “Mun samu bayanan sirri cewa wasu manyan ‘yan jam’iyyar adawa na shirin ɗaukar nauyin ɗalibai da ‘yansiyasa daga wasu jihohin arewa maso yamma don haddasa fitina ta hanyar fakewa da zanga-zangar goyon bayan Sarki Aminu Ado Bayero.

    “Gwamnatin jiha ta haramta zanga-zanga, da kowane irin maci, sannan duk mutumin da aka gani yana aikata hakan za a kama shi nan take.”

    • Me zaman fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado ke nufi?
    • Abin da hukuncin kotu kan rushe masarautun Kano ya ƙunsa
  11. Isra'ila na ci gaba da ruwan wuta a Gaza

    Sojojin Isra'ila na cigaba da luguden bama-bamai a kudancin Gaza, duk da kiran da ake musu na su tsagaita wuta domin daina kashe fararan-hula.

    Algeria ta ce zata aike da wani kudiri MDD na neman a kawo karshen wannan kisa.

    Gwamnatin Washington ta ce tana bibiyan abubuwan da ke faruwa, duk da dai ta nuna goyan-bayan Isra'ila a Rafah, inda take cewa babban farmakin fatatakar 'yan ta'adda ne.

    Sai dai kuma a wani bangaren tace akwai takaici ganin yadda hare-haren jiya Talata suka lakume karin rayuwa fararan-hula a sansanin 'yan gudun hijira da ke yankin Rafah.

    Isra'ila dai ta ce ba ita ta kai wannan harin ba.

  12. Buhari ya roƙi 'yan Najeriya su saka wa gwamnatin Tinubu albarka

    Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Shugaban Ƙasa Bola Tinubu murnar cika shekara ɗaya a kan mulki, yana mai neman 'yan ƙasar su goya wa gwamnatin jam'iyyarsu ta APC baya "don ta yi nasara wajen gina ƙasa".

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon shugaban ya wallafa a shafukan zumunta, Buhari ya kuma nemi 'yan Najeriya "su saka wa gwamnatin ta Tinubu albarka" kuma "su ƙara ƙarfafa haɗin kan ƙasa".

    "Haka nan, Buhari ya yi wa gwamnatin Tinubu fatan gama mulki cikin nasara," in ji Garba Shehu.

    A yau Laraba 29 ga watan Mayu Tinubu ke cika shekara ɗaya da shan rantsuwar kama mulki bayan ya yi nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a zaɓen watan Fabrairun 2023 a ƙarƙashin jam'iyyar APC.

    Muhammadu Buhari ne shugaban ƙasar da ya fara cin zaɓe a APC, inda ya mulki ƙasar daga 2015 zuwa 2023.

  13. 'Yan Afirka ta Kudu sun fara jefa ƙuri'a a babban zaɓe

    A yau ake gudanar da zaben gama-gari a Afrika ta Kudu wanda ake ganin shi ne irinsa mafi tasiri tun bayan kawo karshen mulkin wariya.

    'Yan kasar na nuna fushinsu kan matsalolin cinhanci da rashawa, da karuwar laifuka, da yawan katse lantarki.

    Kazalika, akwai matsalolin karancin ruwan sha da ake ganin za su kasance kalubale ga jam'iyyar da ke mulki, wadda ka iya rasa rinjaye a karon farko cikin shekara 30.

    Wakiliyar BBC a Johannesburg ta ce a farko-farko ana ganin jam'iyyar ANC da ta yi wa kasar fafutikar kawo karshen mulkin wariya za ta rasa rinjayenta, don haka ya zama dole ta kulla haɗaka da jam'iyyun adawa. Kuma a cewarta hakan zai jefa kasar cikin ruɗani.

  14. Maraba

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na ranar Laraba daga BBC Hausa.

    Ku biyo mu don sanin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.