Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/05/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 27 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Umar Mikail and Haruna Kakangi

  1. Gwamnan Kano ya amince da naɗin sabon shugabancin tashar talabijin ta ART

    Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin Hajiya Hauwa Ibrahim, a matsayin mai riƙon shugabancin tashar talabijin ta jihar, ART ( Abubakar Rimi Television).

    Naɗin ya biyo bayan dakatar da Mustapha Indabawa a matsayin manajan darekta na tashar.

    A yau Litinin ne Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Baffa Bichi, ya fitar da takardar naɗin, inda a cikin wasiƙar ya umarci Hajiya Hauwa Ibrahim ta karɓi ragamar jagorancin tashar, nan take.

    Kafin naɗin na yanzu Hajiya Hauwa, ita ce mataimakiyar manajan darektan tashar talabijin ɗin.

    Idan ba a manta ba gwamnatin jihar ta Kano ta shigar da tuhuma bakwai a gaban hukumar yaƙi da rashawa ta jihar, kan shugaban da aka dakatar, da kuma babban jami'in ma'aikata na tashar Ibrahim M. Bello - tuhumar da ta ƙunshi aikata mugun laifi da ɓarna da kuma karkatar da kuɗaɗe.

    Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan ƙorafin da aka rubuta wa gwamnan jihar a kan manajan darektan tashar talabijin ɗin.

  2. Sojoji sun sake buɗe rukunin shagunan Banex a Abuja

    Rundunar sojin ƙasan Najeriya ta tabbatar da sake buɗe rukunin shagunan kasuwanci na Banex da ke unguwar Wuse 2 a Abuja bayan rufe su da aka yi sakamakon wata tashin-tashina, a ranar Asabar, 18 ga watan Mayu, 2024.

    Ranar Lahadi ne kuma 19 ga wata, rundunar sojin ta rufe wajen ne domin gudanar da bincike kan ayyukan da ta bayyana a matsayin na masu aikata ɓarna.

    Kafin rufewar an ga wani bidiyo na yawo a shafukan intanet inda wasu mutane suka far wa wasu sojoji a kusa da rukunin shagunan.

    Bidiyon ya nuna yadda wasu jami'an ƴansanda suka shiga tsakani domin ceton jami'an sojin da mutane suka riƙa kai wa duka da jifa.

    Da yake sanar da sake buɗewar a wata sanarwa a yau Litinin, Darektan hulɗa da jama'a na rundunar sojin Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce matakin sake buɗewar na daga cikin matsayar da aka cimma a taron da aka yi a ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, da shugabannin rukunin shagunan da sauran shugabannin hukumomin tsaro na Abuja.

    Janar Onyema, ya ce daga cikin matakan da aka ɗauka a taron har da rufe shago mai lamba C93, da kuma kama masu shagon da aka yi rikicin.

  3. Kotu ta tabbatar da nasarar gwamnonin Kogi da Bayelsa

    Kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan Jihar Kogi, da ta zauna a Abuja a yau Litinin ta tabbatar da nasarar, dan takarar jam'iyyar APC Usman Ododo.

    Kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Ado Birnin-Kudu, ta yi watsi da ƙarar da Murtala Ajaka, na jam'iyyar SDP ( Social Democratic Party) ya yi saboda gaza tabbatar da gaskiyar ƙorafin da ya shigar na maguɗi a zaɓen.

    Shi kuwa ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC a Jihar Bayelsa kuma tsohon ƙaramin ministan fetur, Timipre Sylva, ya yi watsi da hukuncin kotun zaɓen gwamna da ya tabbatar da nasarar, Douye Diri na jam'iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar.

    Bayan hukuncin kotun da alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Adekunle Adeleye ya sanar, wanda kuma Sylva bai gamsu da shi ba, ya gudanar da taron sirri da manya da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ta APC, inda daga bisani ya ce ya umarci lauyoyinsa da su nufi kotun ɗaukaka ƙara.

    Tun da farko kotun sauraron ƙarar gwamnan da ta yi zamanta a Abuja ranar Litinin ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar gwamnan da kuma jam'iyyarsa ta APC suka shigar, bisa abin da ta kira rashin dacewa.

  4. Benjamin Netanyahu ya yarda Isra'ila ta yi kuskure a Rafah

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce an samu haɗari na ban-tausayi a harin sama da sojojin ƙasarsa suka kai Rafah, wanda ya haddasa gagarumar gobara a sansanin ƴan gudun hijira na Falasdinawa, inda gommai suka mutu.

    Bayan suka da kasashe da hukumomin duniya ke yi Netanyahu ya gaya wa majalisar dokokin ƙasar cewa lamarin ya faru duk da abin da ya kira ƙoarin da suka yi na kauce wa cutar da waɗanda babu hannunsu a faɗan.

    Firaministan ya ce za a gudanar da bincike kan lamarin.

    Hukumomin sojin Isra'ila sun ce an hari wasu manyan ƴan Hamas ne a harin na sama.

    A martaninta fadar gwamnatin Amurka, (White House ), ta buƙaci Isra'ila da ta ɗauki duk wani mataki na kare fararen hula a Gaza.

    Babban jami'in hulɗa da ƙasashen waje na Tarayyar Turai, Josep Borrell, ya buƙaci Isra'ila da ta bi umarnin Kotun Duniya na makon da ya gabata na ta daina kai hari a Rafah.

  5. Rasha za ta fitar da Taliban daga jerin ƙungiyoyin ta'adda

    Rasha ta ce za ta fitar da sunan Taliban daga jerin ƙungiyoyin ƴan ta'adda, kusan shekara uku bayan da ƙungiyar ta masu kirarin jihadi ta sake kama mulki a Afghanistan.

    Ministan harkokin waje na Rasha, Sergei Lavrov, ya ce matakin ya biyo bayan yadda da ainahin al'amuran da ke wanzuwa a yanzu.

    Ita dai Rasha ta ci gaba da alaƙa da Taliban duk da takunkumin da wasu manyan ƙasashen duniya suka sanya wa Taliban ; an gayyaci jami'an gwamnatin Taliban zuwa taron shekara-shekara na duniya na tattalin arziƙi da ake yi a birnin Saint Petersburg da ke Rasha.

    Kamar yadda sauran ƙasashen duniya suka yi a hukumance Rasha ba ta yarda da Taliban a matsayin gwamnatin Afghanistan ba.

  6. Kotu ta umarci Aminu Ado ya daina ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano

    Babbar kotun jihar kano ta umarci sarkin Kano na 15, Mai martaba Aminu Ado bayero da ya daina kira ko gabatar da kansa a matsayin Sarkin Kano.

    Haka kuma kotun ta bayar da umarni ga ƴansanda da su fitar da shi daga fadar Sarkin Kano da ke unguwar Nassarawa a cikin jihar.

    A umarnin da kotun ta bayar bayan da ta karanta bukatar da lauyan gwamnatin jihar Kanon Ibrahim Isa Wangida ya gabatar mata, kotun ta zartar da umarnin na wucin-gadi.

    Bayan Alhaji Aminu Ado Bayero, kotun ta kuma umarci sauran sarakuna hudu da aka rushe da su daina ayyana kansu a matsayin sarakunan masarautun.

    Masarautun da aka rushe dai su ne wadda tsohuwar gwamnatin jihar kanon ta APC karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta kirkiro wato Kano da Bichi da Gaya da Rano da kuma Karaye.

    Wannan dai na zuwa ne bayan da Sarkin na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya gabatar da zaman fada a yau Litinin.

    Babbar kotun ta dage zaman sauraren karar wadda aka shigar a gabanta ranar 24 ga watan nan na Mayu 2024, zuwa ranar 11 ga watan Yuni shekara ta 2024 domin saurare.

  7. ‘Yadda iyayena suka ɓoye cikin awaki don guje wa masu satar mutane'

  8. Yadda Aminu Ado ya yi zaman fada a gidan Sarki na Nassarawa

    Sarkin Kano na 15 a jerin Sarukan Fulanin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi zaman fada a yau Litinin a fadar gidan Sarki da ke Nassarawa.

    Wannan dai na zuwa ne sakamakon saɓata juyata da ake samu tsakanin ɓangarensa da na wanda gwamnatin jihar Kano ta ayyana a matsayin sabon Sarki, Muhammad Sanusi II, bayan rushe masarautun jihar guda biyar da majalisar dokoki ta yi.

  9. Ya kamata a koya wa yara gaskiya da tsare mutuncin kai - Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nemi iyaye da mariƙa su ƙara azama wajen koya wa yaran "gaskiya, da aiki tuƙuru".

    Wannan dai na ɗauke ne a cikin saƙonsa na taya 'yan Najeriya murnar Ranar Yara ta Duniya.

    Wata sanarwa da kakakin fadar shugaban ƙasa Ajuri Ngelale ya fitar ta ce shugaban ya ci alwashin samar wa ƙananan yara makoma nan gaba domin cinmma burukansu na rayuwa.

    Sanarwar ta ce bisa la'akari da ƙara kuɗaɗe a fannin ilimi da gyran tsarin ilimin da aka yi a baya-bayan nan domin samar da yanayin koyo da koyarwa da kuma hukumar kula da Almajiri da yaran da ba sa zuwa makaranta, shugaba Tinubu ya nanata cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da faɗaɗa damarmakin samun ilimi mai nagarta ga dukkannin 'yan Najeriya.

  10. Adadin Isra'ilawan da ke neman zama 'yan Jamus ya ninninka bayan harin Hamas

    Ana ci gaba da samun Isra'ilawan da ke neman takardar shaidar zama Jamusawa tun bayan harin da mayaƙan Hamas suka kai ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

    Kimanin Isra'ilawa 7,000 ne suka nemi fasfo ɗin Jamus a wata hudun farko na wannan shekarar, adadin da ya ninninka idan aka kwatanta da 9,000 kacal suka nemi fasfo din a shekarar 2023 baki daya.

    Jamusawa da suka tsere wa gallazawar gwamnatin wariya ta Nazi a Jamus da zuri'arsu na da 'yancin neman zama 'yan ƙasar a hukumace.

  11. Ya kamata a rushe hukumomin zaɓen jihohi - Ministan Shari'a

    Ministan Shari'a na Najeriya, Lateef Fagbemi ya ce akwai buƙatar rushe hukumomin zaɓe na jihohi waɗanda ya bayyana da babban dalilin da lalacewar al'amura ga ci gaban ƙananan hukumomi.

    Ministan ya faɗi hakan ne yayin wata tattaunawa kan wani maudu'i na Matsalolin tsaro a Najeriya da shugabanci a matakin ƙananan hukumomi ranar Litinin a Abuja.

    Ministan ya ƙara da cewa gwamnoni sun fake kan gazawar sassan tsarin mulkin Najeriya na 1999 wajen kassara ƙananan hukumomi.

    Mista Fagbemi ya ce babban abin da gwamnoni ke amfani da shi wajen daƙile cigaban ƙananan hukumomin shi ne amfani da hukumomin zaɓe na jihohi ta hanyar ɗamfara wa jama'a shugabannin da suke so.

    Minsitan daga ƙarshe ya kuma nuna irin illar amfani da asusun bai ɗaya ga jihohi da ƙananan hukumomi wani abu da ya ce shi ma yana cikin abubuwan da suka illata ƙananan hukumomi ta hanyar riƙe kuɗaɗen da suka kamata su je ga ƙananan hukumomin.

  12. Sai yau Litinin muka karɓi umarnin kotu kan sauke Aminu Ado - Gwamnatin Kano

    Yayin da ake cigaba da dambarwar saukewa da ɗora sabon sarki a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, gwamnatin jihar ta ce sai a ranar Litinin ta samu umarnin da ke hana ta rusa sababbin masarautu huɗu.

    A ranar Juma’a da dare ne Aminu Ado Bayero ya koma Kanon bayan balaguron da ya yi a kudancin Najeriya, inda ya tarar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke shi daga gadon sarautar garin tare da mayar da Muhammadu Sanusi II kan karagar.

    Wannan ta sa Aminu Babba, mai muƙamnin sarkin dawaki babba a masarautar, ya kai ƙara wata kotun tarayya wadda ta ba da umarnin a dakatar da sauke Aminu Ado, da naɗin Sanusi a matsayin sarki, sannan a bar abubuwa a yadda suke har sai ta kammala sauraron ƙarar.

    Sai dai kuma, gwamnatin Kanon ta bakin Kwamashinanan Shari'a Haruna Isa Dederi, ta ce sai bayan sun aiwatar da duk abubuwan da kotun ta hana sannan suka ga umarnin nata.

    "Wannan umarni da ake ta yamaɗiɗi a kai sai a yau [Litnin]...da misalin ƙarfe 10:00 na safe sannan ma'aikacin kotun tarayya a nan Kano ya kawo min shi," in ji shi.

    "Tun da yau ce ranar aiki kuma sai yanzu muka karɓa, to sai a saurari abin da kotun za ta ce idan muka tura namu takardun [martanin]."

    Wakilin BBC a Kano ya yi yunƙurin jin dalilin da ya jawo jinkiirin isar umarnin kotun daga ɓangaren waɗanda suka shigar da ƙara amma bai yi nasara ba.

    Yanzu haka dai Muhammadu Sanusi II na zaman fada a babban gidan sarki na cikin gari, yayin da shi kuma Aminu Ado Bayero ke nasa zaman a gidan sarki da ke unguwar Nasarawa.

    • Abin da hukuncin kotu kan rushe masarautun Kano ya ƙunsa
    • Abu bakwai da Muhammadu Sanusi II ya faɗa lokacin karɓar takardar mulki
    • Ba ni da hannu a rushe sababbin masarautun Kano - Rabiu Kwankwaso
    • Masarautar Kano ta yi fiye da shekara 2000 da kafuwa
  13. Ƙasashe biyar na yankin Sahel suna gudanar da atisayen soji a Nijar

    Dakarun Mali da Nijar da Burkina Faso da Chadi da kuma Togo suna gudanar da wani gagarumin atisayen soji a yammacin Nijar tun ranar 20 ga watan Mayu da nufin karfafa alaka da jama'ar yankin, in ji gidan rediyon Faransa RFI.

    Atisayen, wanda shi ne irinsa na farko a yankin Sahel da aka yi wa lakabi da "Ƙaunar Kasa", zai gudana ne har zuwa ranar 3 ga watan Yuni.

    A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Mali ta fitar a ranar 26 ga watan Mayu ta ce ƙasar Guinea ma za ta shiga atisayen, wanda ma'aikatar tsaron Nijar ta ce ya hada da "hanyoyi" da "tsari da nufin karfafa alaka da al'ummar yankin".

    Ƙasashen Burkina Faso da Nijar da Mali sun kafa ƙawance na ƙasashen yankin Sahel tare da bayyana ficewarsu daga kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka.

    Yankin Sahel dai na fama da tashe-tashen hankula daga mayakan da ke da alaka da al-Qaeda da kungiyar IS.

  14. Hare-haren Isra'ila sun kashe Falasɗinawa 45 a Rafah, in ji ma'aikatar lafiya a Gaza

    Aƙalla mutum 45 ne suka mutu a hare-haren Isra'ila ta sama kan sansanin gudun hijirar Falasɗinawa da ke birnin Rafah a kudancin Zirin Gaza.

    Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce cikin mutanen har da mata da ƙananan yara..

    Bidiyon da aka ɗauka bayan hare-haren na Tal al-Sultan ranar Lahadi da dare sun nuna yadda wuta ta tashi bayan bamabamai sun fashe.

    Rundunar sojin isra'ila ta ce ta kashe shugabannin Hamas biyu kuma tana duba rahotonnin da ke cewa an kashe fararen hula a harin.

    Kafin haka, ƙungiyar ta ce ta harba makaman roka kan birnin Tel Aviv na Isra'ilar - wanda shi ne karon farko da ta kai hari tsakiyar ƙasar tun watan Janairu.

    Lamarin ya faru ne kwana biyu bayan Kotun Manyan Laifuka ta Duniya ta umarci Isra'ilar ta dakatar da farmakin da take kaiwa a Rafah nan take, inda dubun dubatar Falasɗinawa ke samun mafaka.

  15. Wasu ƴan Afrika ta Kudu za su fara kaɗa ƙuri'a kafin ainihin ranar zaɓe

    Tsofaffi da masu buƙata ta musamman za su fara kaɗa kuri'a yau Litinin a babban zaben Afirka ta Kudu da za a yi ranar 29 ga watan Mayu.

    Hukumar zabe za ta kai musu kayan jefa ƙuri'a gidajensu domin su kaɗa kuri'arsu.

    Sauran mutanen da suka zabi kada kuri'a kafin ainihin ranar zaɓen saboda ba za su iya shiga rumfunan zabe ba, su ma za su kada kuri'unsu a yau ɗin.

    Hukumar zaben kasar ta amince da ‘yan kasar Afirka ta Kudu sama da miliyan 1.6 su kada kuri’arsu da wuri kafin ainihin ranar zaɓen.

    Shugaba Cyril Ramaphosa ya fada a wani jawabi ta gidan talabijin ga al'ummar kasar a ranar Lahadi cewa yana sa ran za a gudanar da zaben cikin yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma adalci.

    Ya ce hukumomin tsaro sun shirya tsaf don haka ya bukaci “dukkan jam’iyyu da ‘yan takara da magoya baya da kowane dan Afirka ta Kudu da su guji duk wani mataki da zai kawo cikas ga tsarin babban zaben ƙasar.

  16. Rukunin farko na alhazan Kano sun tashi zuwa Saudiyya

    A yau Litinin ne rukunin farko na alhazan jihar Kano daga arewacin Najeriya suka tashi zuwa Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin bana.

    Gwamna Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Aminu Abdussalam ne suka yi wa alhazan rakiya zuwa filin jirgi, inda gwamnan ya nemi su kiyaye dokokin ƙasar yayin zaman ibadar da suka je yi.

    Rahotonni na cewa alhazai 550 ne suka tashi daga filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke jihar.

  17. Burkina Faso ta tsawaita mulkin soji har zuwa 2029

    Al'ummar Burkina Faso da dama na maraba da matakin da gwamnatin mulkin sojan kasar ta dauka na tsawaita mulkin kasar na tsawon shekaru biyar har zuwa shekarar 2029, kamar yadda gidan talabijin na kasar RTB ya ruwaito.

    An sanar da matakin ne a tattaunawar kasa a ranar 25 ga watan Mayu.

    An kara wa'adin komawa mulkin dimokradiyya da watanni 60 daga ranar 2 ga watan Yuli.

    "Za a iya shirya zabukan da ke nuna kawo karshen mika mulkin soji kafin wannan wa'adin idan har lamarin tsaro ya tabbata," in ji wata sabuwar yarjejeniya da shugaban mulkin soja, Capt Ibrahim Traore ya sanya wa hannu.

    Kyaftin Traore dai ya ƙwace mulki a shekarar 2022 lokacin da ya hamɓarar da wani shugaban mulkin soja, Laftanar Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba.

    • Sojoji sun sake yin juyin mulki a Burkina Faso
    • Yadda ficewa daga Ecowas zai shafi Mali da Nijar da Burkina Faso
  18. An kashe mutum 139 da raunata 930 cikin mako biyu a El-Fashir na Sudan

    Ƙungiyar ba da agaji ta likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce sama da mutum 130 ne suka mutu sannan wasu sama da 930 suka jikkata cikin mako biyu da aka kwashe ana gwabza fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF a garin al-Fashir da ke yammacin ƙasar.

    MSF ta faɗa cikin wani saƙo a shafin X ranar 26 ga watan Mayu cewa daya daga cikin ma'aikatanta na cikin wadanda suka mutu.

    Birnin wanda shi ne mafi girma kuma na ƙarshe a hannun dakarun gwamnati, ya sha fama da tashe-tashen hankali tun daga ranar 10 ga watan Mayu wanda ya raba dubun-dubatar fararen hula da muhallansu sakamakon tabarbarewar yanayin rayuwa.

    Duk kasuwanni sun kasance a rufe saboda cigaba da kai hare-hare ta sama da kuma luguden wuta da bangarorin da ke fada da juna ke yi.

    A ranar 26 ga Mayu Gwamnan Darfuri Minni Minnawi ya zargi dakarun RSF da "kisan ƙare-dangi mafi girma a cikin kankanin lokaci ta hanyar jefa bamabamai kan gidajen fararen hula da asibitoci".

    RSF ta yi watsi da zargin gwamnan kuma a maimakon haka ta zargi sojoji da kungiyoyin da ke dauke da makamai na Darfur da amfani da "farar hula a matsayin garkuwar".

  19. Dattijuwar da ta zaɓi Nelson Mandela yanzu ba ta goyon bayan magadansa

  20. Papua New Guinea na fargabar ɓacewar dubban mutane bayan zabtarewar ƙasa

    Akwai fargabar adadin wadanda suka bace sakamakon zaftarewar kasa a Papua New Guinea ka iya kai dubunnan mutane, in ji wata hukumar gwamnati.

    Mukaddashin daraktan cibiyar bala'o'i ta ƙasar ya ce a cikin wata wasika cewa ana fargabar sama da mutane 2,000 sun ɓace a cikin tarkace a bala'in da ya faru a ranar Juma'a.

    Sai dai kuma, ya yi wuya a iya tantance ainihin adadin mutanen da suka mutu, kuma alkaluma sun bambanta sosai, saboda aikin ceto ya samu cikas a wasu wurare da kuma rashin isassun kayan aiki.

    Ƙasa da gawarwakin mutane goma ne aka gano kawo yanzu, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin wadanda suka bace ya kai 670.

    Rushewar wani tsauni da sanyin safiyar Juma'a ya kawar da wani kauye mai cike da cunkoson jama'a a lardin Enga, inda barnar ta kai kusan kilomita daya, kamar yadda masu lura da al'amura suka bayyana.

    Kimanin mutum 3,800 ne ke zaune a yankin kafin afkuwar lamarin.

    Wasikar da aka rubuta ta ce barnar ta yi yawa, kuma ta "ya haifar da babban tasiri ga ci gaban tattalin arzikin kasar".

    Firaiminista James Marape ya jajantawa tare da bai wa rundunar tsaron kasar da hukumomin gaggawa umarnin zuwa yankin mai tazarar kilomita 600 daga arewa maso yammacin Port Moresby babban birnin kasar.

    • Zabtarewar kasa: Mutum 40 sun mutu ana neman 13 a Kamaru
    • 'Tamkar ambaliyar tsunami ce ta auka wa birnin Libya'