Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/05/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 24 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Umar Mikail and Usman Minjibir

  1. Hotunan ɗakin taron da za a miƙa wa Sarki Muhammadu Sanusi ll takarda

    Shirye-shirye sun yi nisa a Kano dangane da miƙa wa Muhammadu Sanausi ll takardar kama aiki a matsayin sabon sarki.

    Tuni dai ɗakin taro na Afirka da ke cikin gidan gwamnatin jihar, ya ɗauki harama, inda ake tsara kujeru da sauran shirye-shirye domin gudanar da taron.

    Nan gaba a yau ne dai ake sa ran sabon sarkin zai isa Kano a shirye-shiryen karɓar mulki.

    A ranar Alhamis ne dai gwamnan jihar Abba Kabir ya sanar da naɗin Muhammadu Sanusi ll a matsayin sabon sakin Kanon bayan ya sanya hannu kan dokar rushe masarautun jihar da majalisar dokokin jihar ta miƙa masa.

  2. Kotun tarayya ta ce a dakatar da dokar rushe masarautun Kano

    Wata kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin dakatar da rushe masarautun jihar biyar da majalisar dokokin jihar ta yi ranar Alhamis.

    Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ne ya shigar da ƙara a gaban kotun, inda yake ƙalubalantar rushe masarautun da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

    Alƙalin kotun, Mai sharia Liman ya bayar da umurnin dakatar da gwamnatin Kano daga aiwatar da matakin rushe masarautun jihar.

    Alkalin ya kuma ɗage shari’ar har zuwa ranar 3 ga watan Yuni domin sauraron ƙarar da aka shigar a gaban kotun.

    Wannan umarnin na kotun dai na zuwa ne 'yan sa'o'i kaɗan kafin ƙaddamar da Muhammad Sanusi II a matsayin sabon sarkin Kano.

    wamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar ta 2024 bayan da majalisar dokoki ta soke dukkan masarautun jihar biyar da aka ƙirƙira a shekarar 2019.

    Jim kaɗan bayan rattaba hannu a kan dokar ne kuma, gwamnan ya sanar da naɗa Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano na 16, bayan ya sauke Aminu Ado Bayero daga kan kujerar.

  3. Ana sa ran Sarki Muhammadu Sanusi ll zai isa Kano a yau

    Nan gaba a yau ne ake sa ran sabon sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll zai isa Kano a shirye-shiryen da ake yi na karɓar mulkin sarautar Kano.

    Bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa tuni shiri ya yi nisa na tarbar sabon sarkin, wanda kawo yanzu ba a san inda zai zauna ba kafin shigarsa fada.

    Bayanai na cewa sabon sarkin ne zai jagoranci sallar Juma'a a babban masallacin jihar.

    Tuni dai gwamnan ya bai wa sarakunan da aka soke masarautunsu, wa'adin sa'o'i 48 da su fice daga cikin masarautun tare da miƙa duka kadarorin masarautunsu zuwa ga mataimakin gwamnan jihar.

    A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya sanar da naɗin Muhammadu Sanusi ll , a matsayin sabon sarkin Kano bayan da majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar masarautun jihar kwaskwarima tare da soke duka masarautun jihar guda biyar.

  4. Majalisar dokokin Louisiana ta amince da dokar haramta zubar da ciki

    Majalisar dokokin jihar Louisiana a Amurka ta amince da ƙudirin dokar da zai ta ba da damar hukunta duk wanda aka samu da shan maganin zubar da jiki ba tare da izini ba.

    Wannan mataki ya sa a yanzu jihar ta kasance ta farko a Amurka da ke haramta shan waɗannan ƙwayoyi da suka yi fice ko ake yawaita sha domin zubar da jiki.

    Yanzu gwamnan jihar ake jira ya sa wa ƙudirin hannu domin ya zama doka.

    Wakilin BBC ya ce ba wai haramtawa ɗungurumgum ba ne, amma shan waɗannan ƙwayoyi zai kasance sai da uzuri mai ƙarfi kamar cutar ulcer da ɓarin ciki.

    Ƙwayoyin sun haɗa da Mifepristone da Misoprostol wanda daga yanzu duk wanda aka kama da shansu ba tare da izinin likita ba, to za ta fuskanci ɗauri a gidan yari da kuma tarar dubban daloli.

  5. MDD ta ce Sudan na fuskantar barazanar kisan ƙare-dangi

    Mai bai wa Majalisar shawara ta fuskar kare aukuwar irin wannan kisa, Alice Wai-rimu Nde-ritu ta faɗa wa BBC cewa, lamarin ya fi muni a yankin Darfur da ke yammacin kasar, inda dakarun RSF da mayakan da ke taimaka musu ke cin karensu ba babbaka.

    Ta ƙara da cewa sun shaida mata yada ake cin zarafinsu ta hanyar lalata, wuwushe dukiyoyi da sata, kone-kone da fashe-fashe har a kasuwa.

    MDD ta kuma nuna matuƙar damuwa kan fararan-hula sama da miliyan guda da ke makale a El Fasher - birnin na ƙarshe da ke ƙarƙashi ikon sojojin Sudan.

    Misis Nde-ritu ta ce rashin hukunta masu asassa irin wannan rikici a tarihi, shiyasa a kullum abubuwa ke sake rincabewa kasar.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, Hajji babbar rana, kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a dai dai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya, musamman Najeriya da makwabtan ƙasashe.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawar a shafukanmu na sada zumunta.