Nan gaba a ayu ne za a gudanar da bikin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Chadi Mahamat Idriss Deby, bayan lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar 6 ga watan Mayu.
Rantsuwar ce kuma za ta kawo ƙarshen mulkin riƙon ƙwarya da aka shafe shekara uku ana gudanarwa a ƙasar.
Ana sa rana manyan baƙi ciki har da shugabannin ƙasashen duniya ne za su halarci bikin da za a gudanar a N'Djamena, babban birnin ƙasar.
Hukumar zaɓen ƙasar ce ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashen zaɓen shugaban ƙasar bayan da ta ce ya samu kashi 61 na ƙuri'un da aka kaɗa.
Sakamakon da jam'iyyun adawa cikin har da babban abokin hamayyarsa firaminista, Succes Masra suka yi watsi da shi, suna masu iƙirarin cewa akwai kura-kurai a ciki.
A watan Aprilun 2021 ne Mahamat Idriss Deby ya ɗare karagar mulkin ƙasar bayan rasuwar mahaifinsa, Idris Deby Itno, da aka kashe a filin daga lokacin wani gumurzu da 'yan tawaye a arewacin ƙasar.