An yaɗa dubban sauro masu yaƙi da Maleriya a Djibouti
Dubun dubatar sauro, waɗanda aka jirkita wa ƙwayoyin halitta ne aka saki a ƙasar Djibouti, a wani yunƙuri na yaƙi da yaɗuwar nau'in sauro mai yaɗa cutar maleriya.
Sabbin sauron jinsin maza da aka saki waɗanda wani kamfanin kula da halittu na Birtaniya ya samar - na ɗauke da wani sanadari da ke kashe sauro jinsin mata kafin su girma.
Nau'in sauron da aka saki ba ya cizo kuma ba ya cutar da al'imma.
Sauro jinsin mata ne kawai ke cizo tare da sanya wa mutane cutar zazzaɓi.
Wannan karo na farko da aka saki irin waɗannan sauro a yankin gabashin nahiyar Afirka, kuma karo na biyu a faɗin nahiyar Afirka.
Amurka ta ce an yi amfani da irin wannan tsari a Brazil da tsibirin Cayman da Panama da kuma Indiya, kuma ya yi aiki yadda ya kamata.